No menu items!

Sample Page Title

Date:

An tsinci gawar wata malamar sashen Biochemistry na Makarantar Kimiyyar Rayuwa ta Jami’ar Fasaha ta Tarayya (FUT) Minna a Jihar Neja, Dakta (Misis) Adefolalu Funmilola Sherifat da aka yanka a gidanta da ke Unguwar Gbaiko a garin.

Channels TV ta ruwaito cewa shugaban ƙungiyar malaman jami’a (ASUU) a makarantar Farfesa Gbolahan Bolarin ya ce, an gano gawar marigayiyar ne a safiyar Lahadi, 29 ga watan Oktoba, lokacin da mabiya cocin ta suka bi ta gidanta bayan ba a gan ta a lokacin hidimar ibada ba.

Wasu mazauna garin sun ce bayan da aka buɗe ƙofar gidanta, an same ta a cikin jininta kuma an yi mata yankan rago a maƙogwaronta da wuƙaƙe a gefenta. Daga baya hukumomin ‘yan sanda sun ɗauke gawar zuwa ɗakin ajiyar gawa.

KU KUMA KARANTA: An kama waɗanda ake zargi da kashe wata mata, ta hanyar yi mata yankan rago a Gwambe

Kafin rasuwarta, tana zaune tare da wata mai yi mata hidima, amma ta sallami yarinyar a ranar Juma’a, 27 ga Oktoba.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Neja ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba kafin lokacin rubuta wannan rahoto.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...