No menu items!

Sample Page Title

Date:

’Yan sanda a jihar Ogun sun kama wani mai suna Gbenga Kolawole bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekara 16 fyaɗe bayan ta yi tatil da giya.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru da budurwar ne yayin wani taron cika shekara bakwai da wani coci ya shirya a Adubi da ke jihar ranar 6 ga watan Nuwamba.

Kakakin Rundunar ’yan sandan jihar, Omolola Odutola ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abeokuta, babban birnin Jihar.

Omolola ya ambato mahaifiyar yarinyar na cewa ta kai ’yar tata ne wani shagon sayar da giya da ke yanki sannan ta kulle ta a ciki.

KU KUMA KARANTA: Ɗan haya ya yi wa ’yar fasto fyaɗe

Sai dai an ambato ta tana cewa, “A nan ne Gbenga Kolawole, mai shekaru 32 ya yi amfani da damar wajen yi mata fyaɗen.

Sai dai Kakakin ya ce wani mai suna Sunday Ibrahim, mazaunin yankin ne ya yi ram da Gbenga lokacin da yake tsaka da aika-aikar.

“Tuni aka garzaya da wacce aka yi wa fyaɗen asibitin Ore-Ofe domin ta samu kulawar lafiya, yayin da shi kuma wanda ake zargin yanzu haka ya shiga hannu ana ci gaba da bincike a kan shi,” in ji Kakakin ’yan sandan.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...