Karo na 3 a jere, kotu ta ƙi amincewa da buƙatar ba da belin Tukur Mamu kan zargin ta’addanci

0
204
Karo na 3 a jere, kotu ta ƙi amincewa da buƙatar ba da belin Tukur Mamu kan zargin ta'addanci
Malam Tukur Mamu

Karo na 3 a jere, kotu ta ƙi amincewa da buƙatar ba da belin Tukur Mamu kan zargin ta’addanci

Mai shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ƙi amincewa da sabuwar bukatar beli da aka gabatar da sunan Tukur Mohammed Mamu, wanda ake zargi da hulɗa da ‘yan ta’adda.

A hukuncin da ya yanke a ranar Laraba, Mai shari’a Umar ya amince cewa Tukur Mamu yana da matsalar lafiya, amma ya umarci Hukumar Tsaro ta Kasa (DSS) kada ta sake shi, sai dai ta kai shi asibitin da ya dace domin a kula da lafiyarsa yadda ya kamata.

Alkalin ya lura cewa masu gabatar da ƙara sun nuna ƙwazo da jajircewa wajen tafiyar da shari’ar, yana mai cewa ɗaya daga cikin dalilan bayar da beli shi ne idan masu gabatar da ƙara ba sa nuna ƙwazo ba. Tunda a wannan lamari an nuna jajircewa, babu hujjar bayar da beli.

KU KUMA KARANTA: An kama Tukur Mamu, mai shiga tsakani don ceto fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Mai shari’a Umar ya kuma ba da umarni cewa lauyoyin wanda ake tuhuma su zaɓi asibitin da ya fi dacewa da shi, inda za a gaggauta kai shi don samun kulawa.

Haka kuma, ya umarci DSS ta ba Tukur Mamu damar yin hulɗa da Iyalansa.

Leave a Reply