Sule Lamido ya yi barazanar garzayawa kotu kan hana shi sayen fom ɗin takarar shugabancin PDP

0
135
Sule Lamido ya yi barazanar garzayawa kotu kan hana shi sayen fom ɗin takarar shugabancin PDP
Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido

Sule Lamido ya yi barazanar garzayawa kotu kan hana shi sayen fom ɗin takarar shugabancin PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi barazanar kai ƙara kotu bayan kasa samun damar sayen fam ɗin takarar kujerar Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa.

Lamido, wanda ya isa ofishin shugaban jam’iyyar na ƙasa da ke Abuja da safiyar Litinin domin sayen fam ɗin, ya bayyana takaicinsa kan abin da ya kira yunƙurin hana shi cimma burinsa na neman kujerar shugabancin jam’iyyar.

Da yake magana da ’yan jarida a gaban magoya bayansa, tsohon Ministan Harkokin Waje ya jaddada cewa yana shirye sosai ya tsaya takara a babban taron zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba a Ibadan, Jihar Oyo.

KU KUMA KARANTA: Akwai yiyuwar nan gaba kaɗan Ganduje ya dawo jam’iyyar PDP – Sule Lamido

Ya ce zai kai ƙara zuwa kotu idan ba a ba shi damar samun fam ɗin takarar ba.

Lamido ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a shafinsa na Facebook tun da farko, inda ya rubuta cewa:

“Da ikon Allah, yau Litinin, 27 ga Oktoba 2025, da ƙarfe 11 na safe, zan kasance a Wadata Plaza, hedikwatar ƙasa ta jam’iyyarmu ta PDP, domin sayen fam ɗin takarar kujerar Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa.”

Leave a Reply