An yi garkuwa da wasu matan aure 8 a gona a Abuja

0
438

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matan aure takwas a wata gona a ƙaramar hukumar Kuje da ke yankin Babban Birnin Tarayya.

An yi awon gaba da matan auren ne kwanaki kaɗan bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin mataimakin Shugaban ƙaramar hukumar Kwali da wasu mutum shida daga ƙauyen Yewuti.

Wani mazaunin ƙauyen Gwombe da ke masarautar Gwargwada Usman Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin.

Ya ce matan auren suna tsaka da shuka iri ne ’yan ta’adda ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 suka yi musu kawanya suka yi awon gaba da su zuwa inda ba a sani ba.

Wani basarake daga wani ƙauye a masarautar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace matan.

KU KUMA KARANTA: Yadda yaro ɗan shekara 9 ya yi garkuwa da ƴar shekara 5 a jihar Bauchi

“Hakika, huɗu daga cikin matan ’yan gida ɗaya ne,” a cewarsa,

Ya ci gaba da cewa, “ina zargin waɗannan ’yan bindiga da suka yi garkuwa da matan na daga cikin waɗanda suka tsere daga ƙauyen Kabbi da ke makwabtaka da su da suke yawo a cikin daji bayan ’yan bangar Miyetti Allah suka kashe wasu daga cikinsu a ƙarshen mako.”

Babu wani martani daga kakakin rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya, SP Adeh Josephine, kan lamarin.

Leave a Reply