An yi bukin ranar Ngizimawa ta duniya ’11-11′ a Potiskum
– Gwamnan Yobe ya ba da tallafin Naira miliyan 20
Mai martaba Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya CON, ya gudanar da taron ranar Ngizimawa (World Ngizim Day), wanda aka fi sani da 11-11 a fadarsa da ke garin Potiskum.
Shi dai irin wannan taro ana yinsa domin tunawa da al’ummar ƙabilar Ngizimawa, domin raya tarihi da al’adun gargajiya na al’ummar Ngzimawa. An gudanar da taron ne a ranar Asabar, 11/11/2025.
A cikin jawabin mai martaba Sarkin na Potiskum a wajen taron, wanda Muƙaddam na Potiskum ya karanta, ya bayyana dalilin shirya irin wannan taro da cewa, domin sake sanin tarihi da kuma raya al’adun gargajiya na al’ummar Ngzimawa. Ya ce “amman babban maƙasudin shirya taron shi ne don samar da haɗin kai da ƙaunar juna a tsakanin al’umma”.

KU KUMA KARANTA: Shaye-shaye ke rura matsalar tsaro a Yobe — Sarkin Fika
Hon. Alh Aji Yerima Bularafa (Mal Terab na Gujba) kwamishinan Ma’aikatar Samar da Arziƙi da Aikin yi, shi ne ya wakilci Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin Mai Mala Buni na inganta zaman lafiya, haɗin kai, da kuma raya al’adu a faɗin jihar Yobe. Ya yaba wa al’ummar Ngzimawa, saboda gudumawar da suka bayar wajen ci gaban jihar Yobe. Kwamishinan yana mai cewa raya al’adu shi ne ginshiƙin asalin kowace al’umma, da kuma samar da haɗin kai.

Kwamishina Bularafa ya isar da saƙon fatan alheri na Gwamnan, yana mai jaddada muhimmancin bukukuwan raya al’adu wajen inganta fahimtar juna da samar da haɗin kai tsakanin ƙabilu daban-daban a Yobe.
Ya ƙarfafa wa al’ummar Ngzimawa gwiwa da su ci gaba da raya al’adunsu, sannan a ci gaba da neman ilimin zamani, kasuwanci, da kuma bunƙasa harkar noma don ci gaban zuriya masu tasowa.

An yi wasannin gargajiya iri daban-daban a wajen, masu ƙayatarwa, waɗanda suke ƙara bayyana al’adun gargajiya na al’ummar Ngzimawa. Sannan an yi hawan Dawakai.
Manyan baƙi a wajen sun haɗa da sarakunan Fune da na Gudi, da Hakimai da dama. Sannan akwai ɗan majalisa mai wakiltar tsakiyar cikin garin Potiskum, Alhaji Ahmed Adamu BBK. Akwai wakilan mai martaba Sarkin Fika, wakilin Sarkin Tikau da wakilin Sarkin Bade. Waɗanda suke riƙe da sarautun gargajiya na masarautar Potiskum da dama sun halarci taron. Taron ya samu halartar dimbim al’ummar Ngzimawa, maza da mata, yara da manya.

A tattaunawarsa da manema labarai bayan kammala taron, mai martaba Sarkin Potiskum, ya godewa Gwamna Mai Mala Buni, kan haɗin kai da ya ba su wajen gudanar da wannan taro. Sannan ya yi godiya ta musamman game da gudumawar Naira miliyan 20 da ya bayar don a yi wannan taro na 11-11. Mai martaba ya yi godiya ga ɗimbim al’ummar da suka halarci taron, sannan ya yi addu’ar Allah Ya mayar da kowa gida lafiya.










