No menu items!

Sample Page Title

Date:

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 1 da ke Sakatariyar Audu Bako, ta yanke wa wasu ’yan bijilanti biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An dai yanke musu hukuncin ne bayan samunsu da laifin kisan wani matashi ɗan shekaru 17 mai suna Ahmad Musa a unguwar Sabon Titin Panshekara.

Masu laifin sun haɗa da Emmanuel Korau da Eliesha Ayuba Jarmai da Irimiya Thimothy da Auwalu Jafar da Mustapha Haladu.

An dai soma tuhumar ’yan bijilantin da laifuka biyu na haɗin baki da kuma kisan kai, laifukan da suka saɓa da sashe na 97 da 221 na Ƙundin Pinal Kod.

Sai dai a yayin sauraron shari’ar duk sun musanta aikata laifukan da ake zargin su da shi.

A yayin sauraron shari’ar ce lauyan mai ƙara, Barista Lamido Sorondinki ya gabartar wa kotu shaidu biyar.

Shi ma lauyan waɗanda ake ƙara, Barista Ahmad Muhammad ya gabatar wa kotu shaidu shida ciki har da waɗanda ake kara.

Yayin da take yanke hukunci, Alkalin Kotun kuma Babbar Jojin Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki ta bayyana cewa kotun ta gamsu da hujjojin da mai ƙara ya gabartar wa kotu, wanda ta yi amfani da su wajen yanke hukunci.

KU KUMA KARANTA: Yadda ta kasance a shari’ar ɗan China kan zargin kisan da ya yiwa Ummita

Ta bayyana cewa game da laifin kisa, kotun ta yanke wa waɗanda ake ƙara hukuncin kisa ta hanyar rataya. Haka kuma, game da laifin haɗin baki, kotun ta yanke musu hukuncin ɗauri na tsawon shekaru biyu a gidan gyaran hali.

Ana iya tuna cewa, tun a ranar 22 ga watan Janairu 2022 ’yan bijilantin su biyar suka haɗu suka yi amfani da gorori suka yi wa marigayin dukan kawo wuka, da bisani kuma wanda ake ƙara na farko ya yi amfani da wuƙa ya daɓa wa marigayin a wuyansa.

Daga baya ’yan bijilantin suka ɗauki gawar marigayin zuwa ofishinsu da ke Cibiyar Horar da Matasa ta Sani Abacha.

Bayan wani lokaci kuma aka ɗauke shi zuwa ofishin ’yan sanda na Kuntau, wanda su kuma suka kai shi Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammed, inda aka tabbatar da rasuwarsa sakamakon raunukan da ya samu a wuyansa da kuma kansa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...