An yanke wa shugaban cibiyar kula da lafiya ɗaurin rai-da-rai kan yi wa wata yarinya fyaɗe

Wata Kotun hukunta laifukan fyaɗe da rigingimun cikin gida da ke Ikeja ta yanke wa Daraktan Cibiyar kula da Ciwon Kansa, Dakta Olufemi Olaleye, hukuncin ɗaurin rai-da-rai har ninki biyu a gidan yari bisa laifin lalata ‘yar uwar matarsa.

Mai shari’a Rahman Oshodi ya samu Mista Olaleye da laifin lalata da fyaɗe ta hanyar jima’i ga yarinyar.

Gwamnatin jihar Legas ce ta fi shigar da ƙarar mai ɗauke da tuhume-tuhume biyu.

Alƙalin ya ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da gamsassun Olaleye ya aikata laifin.

Mista Oshodi ya ce shaidun da ake tuhumar daraktan gamsassu ne.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *