An tsinci gawar yaro da ruwa ya taho da shi a gadar Nahuta Potiskum

0
232
An tsinci gawar yaro da ruwa ya taho da shi a gadar Nahuta Potiskum
Gawar Abubakar Sadi

An tsinci gawar yaro da ruwa ya taho da shi a gadar Nahuta Potiskum

An yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a yankin Potiskum, a ranar Lahadi. Hakan ya yi sanadiyar mutuwar wani yaro da ruwan ya taho da shi aka tsince shi a gadar Nahuta Potiskum jihar Yobe.

Shi dai yaron ɗan wani ƙauye ne da ake kira Yaɓel, gabar da Baɗejo. Sannan an tsinci gawar ta sa ne a gadar tsakanin Nahuta da Lafiya, kan hanyar zuwa Ngojin.

Neptune Prime ta zanta da ɗaya daga cikin waɗanda suka tsinci yaron a can unguwar Nahuta, mai suna Iliyasu IKD, inda ya bayyana cewa yaron sunansa Abubakar Sadi, shekararsa biyar (5). Kuma tuni mahaifinsa ya zo ya ɗauke shi har an yi masa janaiza.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Jigawa sun kama magidanci ɗan shekara 70 kan zarginsa da kashe ‘yar’uwarsa 

Mahaifin yaron ya shaida mana cewa, yaron ya fita wasansa a waje, sai aka fara ruwan sama mai ƙarfi, muka ga shiru bai dawo ba. Duk inda muka duba bayanan. Ashe ruwan ne ya tafi da shi. Sai muka ji ana sanarwa an tsinci gawar yaro a gadar Nahuta, da muka zo kuwa sai muka ga shi ne.

Leave a Reply