No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnati ta sake bayar da umarnin rufe wasu Asibitoci masu zaman kansu guda 6 da suke gudanar da ayyukan kula da lafiyar jama’a ta haramtacciyar hanya a Jihar Oyo.

Umarnin rufe Asibitocin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiyar jihar ta aika wa kafofin labarai a ranar Alhamis.

Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske a Ibadan, babban birnin jihar, Shugaban Hukumar Yaƙi da Asibitocin Bogi, Dokta Adekunle Aremu, ya ce an gano cewa Asibitocin shida da aka rufe suna horas da mutanen da ba su da ilimi da kwarewa a kan aikin kiwon lafiya kuma suke gudanar da ayyuka a matsayin likitoci da ma’aikatan jinya.

Ya ce an ɗauki matakin rufe Asibitocin ne domin tabbatar da manufar gwamnati ta kare lafiyar al’umma a jihar.

KU KUMA KARANTA: Likitan bogi da ya ɗinke mahaifa da mafitsarar wata mace ya shiga hannu

Dokta Aremu ya ƙara da cewa za a hukunta dukkan waɗanda aka samu da karya dokar kiwon lafiya a jihar.

Ya roƙi jama’a da su taimaka wajen bayar da gudunmawar tona asirin irin waɗannan Asibitocin bogi ta hanyar miƙa rahoto ga mahukunta.

Ya shawarci jama’a da su yi wa kansu karatun-ta-nutsu ta fannin yin amfani da halastattun Asibitoci da ɗakunan shan magani da suke da ƙwararrun ma’aikata domin kare kansu daga faɗawa hannun bara-gurbin ma’aikata.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Asibitocin da aka rufe sun haɗa da New Jobi Memorial Hospital da Omolara Clinic and Maternity Home da Amazing Grace Medical Clinic da Emiloju Clinic and Maternity Center da Safeway Clinic da Emilagba Clinic and Maternity Center.

Neptune Hausa ta ruwaito cewa a kwanan baya ma ma’aikatar lafiyar jihar ta bayar da irin wannan umarni ga wasu Asibitoci masu zaman kansu da aka kama likitocin bogi suna ikin tiyata ba tare da ƙwarewa ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...