An sace mahaifin mataimakin shugaban ƙaramar hukuma a Abuja

Daga Haruna Idi Hassan

Ƴan ɓindiga sun sace mahaifin mataimakin Shugaban ƙaramar Hukumar Kwali dake babban birnin tarayya, Mohammed Yakubu da wasu mutum shida.

Rahotanni sun ce maharan sun harɓe wani mutum, sannan suka yi awon gaba da wata mai juna biyu da wasu mutum biyar a ƙauyen Yewuti da ke ƙaramar hukumar.

Aminiya ta ruwaito cewa mahara sun taɓa kai hari ƙauyen a ranar watan Afrilu, suka sace mutum 29.

Da yake tabbatar da afƙuwar lamarin, wani mazaunin garin Ibrahim Danjuma ya ce da misalin ƙarfe 12 na safe maharan ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 suƙa mamaye wasu gidaje uku ciki har da na mahaifin mataimakin shugaban, suka tafi da shi tare da wasu mutane shida.

KU KUMA KARANTA: An cafke matar da ta sace ’yar shekara 3 a Neja

Ya ƙara da cewa, “’yan bindigar sun harɓe ɗaya daga cikin mutanen ƙauyen, Hussaini Kure, wanda ya yi yunƙurin tserewa.”

Basaraken yankin, Etsu Yewuti, Mohammed Isyaku, wanda ya ce al’ummar yanƙinsun firgita da harbi da ’yan bindigar suka yi ya roƙi mahuƙunta da su taimaka wa talakawansa wajen gain jami’an tsaro sun ƙuɓutar da waɗanda aka sace.

Ya ce, “ƙaro na uƙu ke nan wannan abin baƙin ciki da damuwa ke faruwa a al’ummarmu. Ina ƙira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa da su kawo mana agaji domin ceto waɗanda aka sace ciki har da wata mace mai juna biyu.”

A halin da ake ciki ’yan bindigar sun buƙaci a biya su kuɗin fansa naira miliyan 30.”

Kaƙakin ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, ta ce tana coci lokacin da aka ƙira ta game da faruwar lamarin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *