Connect with us

Labarai

An sace ɗalibai ‘yan makaranta 1,683 cikin shekaru 8 a Najeriya – Rahoto

Published

on

Wani rahoto da ƙungiyar ‘Save the Children International’ (SCI) ta fitar, ya bayyana cewa an kai hari kusan makarantu 70 tare da yin garkuwa da yara ‘yan makaranta 1,683 a faɗin Najeriya tsakanin watan Fabrairun 2014 zuwa Disamba 2022.

Rahoton mai taken, “Ilimin da ake kai wa hari: Bita da nazari kan hare-haren da aka kaiwa Makarantu, Malamai, da Almajirai daga sace ‘yan matan Chiɓok, a jihar Borno, Nigeria a 2014.”

Mashawarcin wanda ya ƙirƙiro rahoton, Augustine Mamedu, yayin da yake gabatar da sakamakon a Abuja ranar Alhamis, ya kuma ce an kashe ɗalibai 184 yayin da wasu 88 suka jikkata a cikin wannan lokaci.

Mista Mamedu ya ƙara da cewa an kuma yi garkuwa da malamai kusan 60 da wasu ma’aikatan makarantar; An kashe 14, yayin da aka lalata gine-ginen makarantu 25.

Ya yi nuni da cewa, tun bayan aukuwar lamarin na Chiɓok a watan Fabrairun 2014 da aka yi garkuwa da ‘yan mata kimanin 276, ana samun ƙaruwar satar mutane.

KU KUMA KARANTA: Bayan Shekaru tara, Sojoji sun sake kuɓutar da ‘yar makarantar Chiɓok guda ɗaya

Ya ƙara da cewa rahotannin sun kuma bayyana cewa an samu sauyin yanayi na sace ɗalibai daga Arewa maso Gabas zuwa shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Ya ce a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2022 an kai hari a makarantu biyar a Arewa maso Gabas, 49 a Arewa maso Yamma, 11 a Arewa ta Tsakiya, uku a Kudu maso Kudu, biyu a Kudu maso Yamma.

“Rahoton ya kuma nuna cewa an kai hare-hare kan makarantu 28 a jihar Kaduna a cikin wannan lokaci, inda aka kai wa makarantu 17 hari a ƙaramar hukumar Kajuru kaɗai.

“A jihar Katsina, an rufe makarantu 99, wanda ya shafi ɗalibai 30,870,” in ji shi.

Mashawarcin ya ce rahoton ya ba da shawarar ƙara zuba jari a makarantu masu aminci da aiwatar da tsarin SSD a duk faɗin ƙasar da kuma rufe wuraren kwana da ke cikin al’ummomin da ba su da wuraren tsaro.

Daraktan ƙasar, SCI, Famari Barro, ya yi ƙira ga cikakken aiwatar da sanarwar ‘Safe Schools’, SSD, da aka sanya wa hannu a cikin 2015 don kare yara ‘yan makaranta daga sacewa da sauran munanan ɗabi’u.

Mista Barro ya bayyana cewa SSD wani alƙawari ne na siyasa da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi don kare yara, malamai da wuraren makaranta daga hare-hare da amfani da kayan makaranta a lokacin rikici na makamai.

Ya ce a duniya ana ci gaba da kai hare-hare kan ilimi, makarantu, yara, da malamansu da kuma yadda jami’an tsaro ke amfani da kayayyakin makaranta a lokacin rikici.

Ya tunatar da cewa gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakai ta hanyar shigar da SSD a cikin gida kuma ta yi alƙawarin aiwatar da ƙa’idodin sanarwar.

Daraktan na ƙasar, ya ce duk da ƙoƙarin da ake yi, hare-haren da ake kai wa harkokin ilimi ya kasance ƙalubale a ƙasar.

Ya bayyana cewa SCI ta ƙaddamar da binciken ne domin duba hare-haren da ake kaiwa makarantu, malamai, da ɗalibai a Najeriya tun bayan harin da aka kai garin Chiɓok a shekarar 2014.

Ya ce an ɗauki matakin ne domin nemo hanyoyin da za a bi wajen ganin an shawo kan al’ummar da abin ya shafa, malamai, da ɗaliban.

Mista Barro ya yaba da kafa cibiyar ba da amsa ga makarantu ta ƙasa, NSSRCC. “Shirin wani mataki ne mai kyau na samar da ingantaccen yanayin koyo ga ‘yan mata, maza da yara masu naƙasa a cikin yanayi na tashin hankali.

“Duk da haka, har sai yaran da ke ƙauyuka masu nisa, waɗanda ke jin barazanar yawan tashin hankali za su iya zuwa makaranta ba tare da tsoro ba, har yanzu da sauran rina a kaba.

“Akwai buƙatar a ƙara yin aiki don hana kai hare-hare, amma kuma a tallafa wa yara da iyalansu, musamman tare da kula da raunuka,” in ji shi.

Da yake mayar da martani, babban sakatare na ma’aikatar ilimi, Andrew Adejo ya bayyana ƙudurin ma’aikatar na tabbatar da tsaro ga kowane yaro ta hanyar aiwatar da SSD.

Mista Adejo, wanda ya samu wakilcin Joseph Achede, mataimakin darakta a fannin ilimin sakandare, ya ce ma’aikatar tana bakin ƙoƙarinta wajen ganin an shawo kan matsalar.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Yarinyar da aka sace a Kogi mai shekaru 16 an same ta a Imo | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

'Yansanda

An tuɓe wa ’yan sanda 5 kaki kan karɓar cin hanci

Published

on

An tuɓe wa ’yan sanda 5 kaki kan karɓar cin hanci

An tuɓe wa ’yan sanda 5 kaki kan karɓar cin hanci

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta tube wa wasu jami’an ta biyar kaki sakamakon zargin su da karɓar cin hancin kuɗi kimanin Naira miliyan uku.

Mataimakin Shugaban ’yan Sanda mai kula da Shiyya ta shida ta da ke Jihar Kuros Riba, Jonathan Towuru, ya sanar a Kalaba cewa ’yan sandan sun kwace kuɗin ne da bakin bindiga a hannun wani mai abin hawa.

A makon jiya ne aka zargi jami’an da ƙwayar kuɗin da bakin bindiga a hannun wani mutum da rundunar ta sakaya sunansa.

Yanzu haka waɗanda ake zargin an tuɓe masu kaki amma ana tsare da su ana bincike, da zarar an same su da laifi kotu za a turasu ta yanke masu hukuncin da ya dace.

KU KUMA KARANTA: ’Yan sanda za su tantance ’yan banga a Yobe

Mataimakin shugaban ’yan sandan ya ce waɗanda ake zargin su da karɓar cin hancin kuɗi Naira milyan uku daga wannun wani.

Ko a kwanan baya irin haka ta taba faruwa a kan babbar hanyar Kalaba zuwa Ikom inda aka kama wasu ’yan sanda kan karbar na goro.

Tafiya a kan hanyar na yawan zargin ’yan sanda da kula da shingen bincike a kan hanyar da yawan tatsar su kuɗi.

Continue Reading

Labarai

Ƙaramar Hukumar Kwami ta kafa kwamitin tsaro saboda rikicin manoma

Published

on

Ƙaramar Hukumar Kwami ta kafa kwamitin tsaro saboda rikicin manoma

Ƙaramar Hukumar Kwami ta kafa kwamitin tsaro saboda rikicin manoma

A ƙoƙarinsa na kauce wa rikicin manoma da makiyaya da ke yawan faruwa a lokacin damuna, Shugaban Karamar Hukumar Kwami a Jihar Gombe, Dakta Ahmed Wali Doho, ya kafa kwamitin tsaro da sanya ido kan ɓangarorin.

Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke garin Malam Sidi, shugaban karamar hukumar, ya bukaci manoma da su guji noma burtalolin shanu, wanda hakan ke haifar da rikici tsakaninsu da makiyaya, da ke haifar da asarar rayuka.

Su ma makiyayan ya gargade su da cewa su guji shiga gonakin manoma, saboda hakan ne ke jawo rikici idan suka cinye musu amfanin gona.

A cewarsa, lokacin girbi me aka fi samun rikicin manoma da makiyayan, saboda haka kwamitin zai ci gaba da sa ido daga yanzu har zuwa lokacin girbin don ganin ba a samu rikici ba.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Yusuf ya amince da sayen taki na naira biliyan 5 don manoman Kano

Ya ƙara da cewa, kusancin garin Kwami da rafi ya sa ya zama wuri mai kyau don noman rani.

Don haka ya ja hankalin manoman yankin da su yi amfani da wannan damar wajen bunkasa tattalin arzikinsu.

Ya jaddada cewa noman rani na da matukar muhimmanci wajen magance matsalar karancin abinci a Najeriya.

Hakan ne ya sa suka haɗa kan matasan yankin don su fara noman rogo da zai taimaka wajen shawo kan matsalar ƙarancin abinci da rage wa manoma tsadar takin zamani.

Continue Reading

Labarai

’Yan sanda za su tantance ’yan banga a Yobe

Published

on

’Yan sanda za su tantance ’yan banga a Yobe

’Yan sanda za su tantance ’yan banga a Yobe

Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta ƙaddamar da shirin yin gyara da kuma tantance ’yan banga domin kawar da ɓata-garin cikin

Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta ƙaddamar da shirin yin gyara da kuma tantance ’yan banga domin kawar da bata-gari a cikinsu.

Kwamishin ’yan sandan jihar, Garba Ahmed, ya sanar da shirin bayan an kama wasu ’yan banga uku da aikata manyan laifuka.

Ya jaddada muhimmancin sake duba ayyukan ’yan banga a jihar, duk da  muhimmiyar rawar da suke takawa wajen taimaka wa jami’an tsaro a yaki da miyagun laifuka.

Ya ce yin gyaran da kuma tantancewa ya zama dole sakamakon ƙorafe-ƙorafen neman yin hakan daga jama’a.

Ya bayyana cewa jama’a sun yi ƙiran ne bayan kama wasu ’yan banga uku da laifin hada baki wajen shiga gida, sata, ƙwace da kuma sayar da kayan sata a Damaturu.

Wata sanarwa da DSP Dungus Abdul Karim, kakakin rundunar, ya fitar, ta ce wasu daga cikin ’yan banga sun kai korafi bayan faruwar lamarin.

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe mutum 12 a Kaduna, sun kai hari a ofishin ƴan sanda a Zamfara

“A ranar 27 ga watan Yuni, 2024, rundunar ta amsa kiran wani mai shago a Damaturu, wanda ya dauki ’yan banga aikin gadi, amma suka kwashe kayan shagon na makudan kudade ba tare da bayani ba.

“Bincike ya kai ga kama wasu mutane biyu da kayan sata da ake zargin sun saya ne daga wani dan banga wanda nan take aka kama shi.

“Ana shawarta jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen daukar masu gadi, sannan su kai rahoton ’yan banga da aka ga suna aikata laifi a bakin aikinsu.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, rundunar tana ɓullo da tsare-tsare don daukar bayanan ’yan banga domin sa ido kan ayyukansu.

Ta ci gaba da cewa ofisoshin ’yan sanda na yankuna da ke jihar za su jagoranci wannan aikin tantancewan domin kawar da baragurbi a cikin ’yan banga.

“Don  haka ake ƙira ga jama’a da su ci gaba da tallafa wa ’yan sanda wajen jainrahoton ayyukan jami’an tsaron da ba su dace ba a hedkwatar jihar ta lamba 07068858500, ko kuma a gabatar da wasikar korafin ga kwamishinan ’yan sanda  ta hanyar kakakin rundunar,” in ji sanarwar.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like