An sace ɗalibai ‘yan makaranta 1,683 cikin shekaru 8 a Najeriya – Rahoto

Wani rahoto da ƙungiyar ‘Save the Children International’ (SCI) ta fitar, ya bayyana cewa an kai hari kusan makarantu 70 tare da yin garkuwa da yara ‘yan makaranta 1,683 a faɗin Najeriya tsakanin watan Fabrairun 2014 zuwa Disamba 2022.

Rahoton mai taken, “Ilimin da ake kai wa hari: Bita da nazari kan hare-haren da aka kaiwa Makarantu, Malamai, da Almajirai daga sace ‘yan matan Chiɓok, a jihar Borno, Nigeria a 2014.”

Mashawarcin wanda ya ƙirƙiro rahoton, Augustine Mamedu, yayin da yake gabatar da sakamakon a Abuja ranar Alhamis, ya kuma ce an kashe ɗalibai 184 yayin da wasu 88 suka jikkata a cikin wannan lokaci.

Mista Mamedu ya ƙara da cewa an kuma yi garkuwa da malamai kusan 60 da wasu ma’aikatan makarantar; An kashe 14, yayin da aka lalata gine-ginen makarantu 25.

Ya yi nuni da cewa, tun bayan aukuwar lamarin na Chiɓok a watan Fabrairun 2014 da aka yi garkuwa da ‘yan mata kimanin 276, ana samun ƙaruwar satar mutane.

KU KUMA KARANTA: Bayan Shekaru tara, Sojoji sun sake kuɓutar da ‘yar makarantar Chiɓok guda ɗaya

Ya ƙara da cewa rahotannin sun kuma bayyana cewa an samu sauyin yanayi na sace ɗalibai daga Arewa maso Gabas zuwa shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Ya ce a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2022 an kai hari a makarantu biyar a Arewa maso Gabas, 49 a Arewa maso Yamma, 11 a Arewa ta Tsakiya, uku a Kudu maso Kudu, biyu a Kudu maso Yamma.

“Rahoton ya kuma nuna cewa an kai hare-hare kan makarantu 28 a jihar Kaduna a cikin wannan lokaci, inda aka kai wa makarantu 17 hari a ƙaramar hukumar Kajuru kaɗai.

“A jihar Katsina, an rufe makarantu 99, wanda ya shafi ɗalibai 30,870,” in ji shi.

Mashawarcin ya ce rahoton ya ba da shawarar ƙara zuba jari a makarantu masu aminci da aiwatar da tsarin SSD a duk faɗin ƙasar da kuma rufe wuraren kwana da ke cikin al’ummomin da ba su da wuraren tsaro.

Daraktan ƙasar, SCI, Famari Barro, ya yi ƙira ga cikakken aiwatar da sanarwar ‘Safe Schools’, SSD, da aka sanya wa hannu a cikin 2015 don kare yara ‘yan makaranta daga sacewa da sauran munanan ɗabi’u.

Mista Barro ya bayyana cewa SSD wani alƙawari ne na siyasa da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi don kare yara, malamai da wuraren makaranta daga hare-hare da amfani da kayan makaranta a lokacin rikici na makamai.

Ya ce a duniya ana ci gaba da kai hare-hare kan ilimi, makarantu, yara, da malamansu da kuma yadda jami’an tsaro ke amfani da kayayyakin makaranta a lokacin rikici.

Ya tunatar da cewa gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakai ta hanyar shigar da SSD a cikin gida kuma ta yi alƙawarin aiwatar da ƙa’idodin sanarwar.

Daraktan na ƙasar, ya ce duk da ƙoƙarin da ake yi, hare-haren da ake kai wa harkokin ilimi ya kasance ƙalubale a ƙasar.

Ya bayyana cewa SCI ta ƙaddamar da binciken ne domin duba hare-haren da ake kaiwa makarantu, malamai, da ɗalibai a Najeriya tun bayan harin da aka kai garin Chiɓok a shekarar 2014.

Ya ce an ɗauki matakin ne domin nemo hanyoyin da za a bi wajen ganin an shawo kan al’ummar da abin ya shafa, malamai, da ɗaliban.

Mista Barro ya yaba da kafa cibiyar ba da amsa ga makarantu ta ƙasa, NSSRCC. “Shirin wani mataki ne mai kyau na samar da ingantaccen yanayin koyo ga ‘yan mata, maza da yara masu naƙasa a cikin yanayi na tashin hankali.

“Duk da haka, har sai yaran da ke ƙauyuka masu nisa, waɗanda ke jin barazanar yawan tashin hankali za su iya zuwa makaranta ba tare da tsoro ba, har yanzu da sauran rina a kaba.

“Akwai buƙatar a ƙara yin aiki don hana kai hare-hare, amma kuma a tallafa wa yara da iyalansu, musamman tare da kula da raunuka,” in ji shi.

Da yake mayar da martani, babban sakatare na ma’aikatar ilimi, Andrew Adejo ya bayyana ƙudurin ma’aikatar na tabbatar da tsaro ga kowane yaro ta hanyar aiwatar da SSD.

Mista Adejo, wanda ya samu wakilcin Joseph Achede, mataimakin darakta a fannin ilimin sakandare, ya ce ma’aikatar tana bakin ƙoƙarinta wajen ganin an shawo kan matsalar.


Comments

One response to “An sace ɗalibai ‘yan makaranta 1,683 cikin shekaru 8 a Najeriya – Rahoto”

  1. […] KU KUMA KARANTA: An sace ɗalibai ‘yan makaranta 1,683 cikin shekaru 8 a Najeriya – Rahoto […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *