An kori Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar APC a mazaɓarsa

0
130

Daga Idris Umar, Zariya

Jam’iyyar APC reshen mazabar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta sanar da dakatar da Abdullahi Umar Ganduje

Mai bai wa Jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazabar Ganduje Hon. Halliru Gwanzo ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

KU KUMA KARANTA: Ba mu da shirin haɗe wa da jam’iyar APC – ‘Yan Kwankwasiyya

Halliru Gwanzo ya ce sun yanke shawarar dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ne sakamakon zarge-zargen da gwamnatin jihar Kano ta yi masa na karbar cin hanci.

Sun ce dakatarwar ta fara ne daga yau 15 ga Afrilu.

Sauran bayani na nan tafe.

Leave a Reply