An kashe Uwargida da Amarya a Kano, an ƙone gawar ɗaya daga cikinsu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Wasu da har yanzu ba a san ko su waye ba sun yi ajalin Uwargida da Amarya, tare da bankawa gawarsu wuta a Unguwar Tudun Yola dake ƙaramar hukumar Gwale a birnin Kano.
KU KUMA KARANTA: Ana zargin Amarya da yiwa angonta yankan Rago a Kano
Mai gidansu, Alhaji Ashiru Shu’aibu ya ce ɓatagarin da ba akai ga gano su ba, sun shiga cikin gidansa, inda suka yiwa matan nasa kisan gilla, sannan suka ƙone gawarsu.
Za a ji cikakken labari daga baya.










