An kashe ɗalibi a kan budurwa a jami’ar FUDMA da ke Katsina

0
651

An kashe wani ɗalibi saboda bambancin addininsa da na budurwarsa, a wani rikicin soyayya a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma da ke Jihar Katsina, kamar yadda Jaridar Aminiya ta wallafa.

Ana zargin wasu ɗalibai ne suka yi wa wani ɗalibi Musulmi, Abubakar Nasir Barda, da ke aji biyu a jami’ar, dukan kawo wuƙa da sanduna har ya ce ga garinku nan, a ƙoƙarin na raba shi da wata budurwarsa Kirista.

Aminiya ta gano wani ɗalibi Kirista a jami’ar da ke son budurwar ne da abokansa suka yi wa Abubakar kisan gilla, ta hanyar dukan kawo wuƙa a ɗakin kwanan ɗalibai, aka kwashe shi zuwa asibitin da ke cikin jami’ar, inda rai ya yi halinsa.

Wakilinmu ya samu labari cewa bambancin addini ya yi tasiri a wajen rikicin, domin kuwa, waɗanda ake zargi da kisan sun yi iya ƙoƙarinsu na raba soyayyar ita Alloysious da Abubakar kasancewar addinin su ba ɗaya ba, amma ta ƙi sauraren su.

KU KUMA KARANTA: Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutane biyar a tsakiyar Somaliya

Kwafin sanarwar da Muƙaddashin Daraktan Tsaron makarantar, Abdulkarim Yahaya ya aike wa shugaban jami’ar a ranar 29 ga watan Satumba, 2023 ta ce ɗalibar da ake rikici a kanta da wasu ɗalibai maza biyar da ake zargi suna tsare a hannun rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Aliyu Abubakar Sadiq ya shaida wa wakilinmu cewa rundunar na bincikar duk waɗanda ake zargin kuma akwai alamun bambancin addini ya yi tasiri a cikin lamarin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Aliyu Abubakar Musa ya yi ƙira da jama’a su kwantar da hankalin su kuma a ci gaba da bin doka da oda.

Ya kuma roƙi duk wani mai wani bayani a kan lamarin da ya yi ƙoƙarin sanar da hukuma kuma za a ba shi kariya ta hanyar ɓoye sunansa da sauran makamantan haka.

Maihaifin marigayi Abubakar, Malam Nasiru Ibrahim Barda, ya nemi da a bi masa haƙƙin ɗansa tare da hukunta duk wani mai hannu a wajen kashe shi.

Leave a Reply