No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yan sanda ta cafke wani mutum da ake zargi da shaƙe wuyan Budurwarsa mai ciki ta mutu har Lahira a jihar Kano. An tsinci matar mai shekaru 22 da haihuwa a sume a bakin titin Kano zuwa Jos a ƙauyen Anadaria, daga bisani kuma ta mutu a Asibiti.

Wanda ake zargin mai suna Ibrahim, ya aikata laifin ne a ƙaramar hukumar Tudun-Wada, kuma an kama shi ne tare da abokin karawarsa mai suna Gabriel Bila da ke Unguwar Korau ƙaramar hukumar Tudun-Wada a jihar Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano (PPRO), Mamman Dauda, ​​ya bayyana kama waɗanda ake zargin a ranar Lahadi, 2 ga Afrilu, 2023.

KU KUMA KARANTA: Yadda matashi ya kashe budurwarsa bayan ya mata ciki a Kano

Dauda ya bayyana cewa wadda aka kashe ta taso ne daga Nasarawan Kuki zuwa ƙauyen ‘Yantomo da ke Kano a ranar Litinin 27 ga watan Maris a lokacin da aka kai mata hari.

“A ranar 2 ga Afrilu, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, mun samu labari daga wani Basamariye nagari cewa an ga wata mace kwance a sume a hanyar Kano zuwa Jos a ƙauyen Anadaria.

Da samun labarin, sai tawagar ‘yan sanda suka garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai yarinyar zuwa babban Asibitin Tiga inda likita ya tabbatar da rasuwarta.”

“A binciken da ake yi, an gano cewa wanda aka kashe ɗin ta bar Nasarawan Kuki zuwa ƙauyen ‘Yantomo da ke ƙaramar hukumar Garin Babba a Kano a ranar 27 ga Maris da misalin ƙarfe 6 na yamma.

An kama babban wanda ake zargin kuma ya amsa laifin yin amfani da mayafin wanda aka kashe ɗin ya shaƙe mata wuya.” Kakakin ‘yan sandan ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...