An kama mutane huɗu da ake zargi da fashin banki a Benuwe, wanda ya yi sanadin mutuwar DPO da ‘yan sanda uku

0
220

A ranar Asabar, 21 ga watan Oktoba, jami’an tsaro na haɗin gwiwa da suka haɗa da jami’an ‘yan sandan Najeriya, da na sojojin Najeriya da dai sauransu, sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a fashin bankin Benuwe da ya yi sanadin mutuwar wasu jami’an ‘yan sanda a kan hanyar Otukpo- Taraku a jihar Binuwai.

Wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa jaridar Punch cewa; “Jami’an tsaro na haɗin gwiwa sun kama wasu ‘yan fashi da makami huɗu a kan hanyar Otukpo-Taraku, jihar Benuwe a ranar Asabar. 

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari kan bankuna a Benuwe, sun kashe mutane takwas

‘Yan fashin na daga cikin ‘yan fashi da makami da suka kai hari a bankuna da ofishin ‘yan sanda a Otukpo a jihar Binuwai.”

Da aka tuntuɓi jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, SP Catherine Anene, ta buƙaci manema labarai da su jira kammala binciken da rundunar ta ke gudanar.

Leave a Reply