An kama marar lafiyan da ya sace motar ɗaukar gawa a Asibiti

2
439

Wani majinyaci da ke kwance a Asibiti a Kano, ya saci motar ɗaukar gawa ya tsere da ita, amma a ƙarshe an kama shi. ‘Yan sanda sun kama ɓarawon motar ne a ƙauyen Takwasa a Jihar Jigawa. Marar lafiya dai yana fama ne da karaya a ƙafarsa, amma har ya samu damar sace motar ɗaukar marasa lafiya da magungunan da ke a jihar Kano.

‘Yan sanda sun kama ɓarawon motar ɗaukar marasa lafiyan ne a ƙauyen Takwasa na ƙaramar Hukumar Ɓaɓura ta jihar Jigawa a yayin da yake ƙoƙarin tserewa da ita.

An kama wani mutum da laifin lalata ‘yar shekara 11 a Anacha

Jaridar Aminiya ta ruwaito Kakakin ‘yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, ya ce “Yan sanda sun gano motar ce a ƙauyen Takwasa ta ƙaramar Hukumar Ɓaɓura a jihar Jigawa, a hannun wani mutum ɗan asalin ƙaramar Hukumar Daura ta jihar Katsina, mai muguwar karaya a ƙafarsa.”

Ya ce an yi nasarar gano motar ce bayan samun rahoton, “sace wata motar ɗaukar marasa lafiya ƙirar ‘Hummer Bus’ marar lamba a jikinta da magungunan da ke cikinta, mallakin ƙaramar Hukumar Ungogo ta jihar Kano, a ƙauyen Kanya Hore da ke ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano.

Daga nan ne ‘yan sanda daga babban ofishin ‘yan Sanda da ke ƙaramar Hukumar Ɓaɓura ta jihar Jigawa suka duƙufa aiki, inda washegari suka gano ta da misalin ƙarfe 8 na safiyar ranar Litinin 11 ga watan Disamban da muke ciki.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kafın a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

2 COMMENTS

Leave a Reply