An kama fasto kan safarar yaran arewa zuwa kudancin Najeriya

0
136

’Yan sanda a Abuja sun kama wani fasto da wasu mutane biyu bisa zargin safarar ƙananan yara daga Jihar Nasarawa zuwa Jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Da yake gabatar da wanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Benneth Igweh, ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma’a bayan da da farko ’yan sandan sun kama wani direban wata motar haya dauke da yaran 12, maza huɗu da mata takwas.

Kwamishinan ’yan sandan ya ce an kwaso yaran masu shekaru 5 zuwa 16 ne daga Akwanga  a Jihar Nasarawa zuwa wani wuri da aka gano daga baya cewa Jihar Ogun ne.

A cewarsa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa dukkan yaran sun fito ne daga Karamar Hukumar Akwanga, kuma wani Fasto Simon Kado da Jesse Simon Kado da yanzu haka suna hannun ’yan sanda ne ke safarar su.

KU KUMA KARANTA: Hukumar ‘yan Sanda ta kama wadda ake zargin sace yara 15 a jihar Ribas

“Kuma yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, rundunar tana ƙoƙarin ganin ta miƙa wa rundunar ’yan sandan jihar Nasarawa yaran domin haɗa su da iyalansu,” in ji shi.

CP Benneth Igweh ya jaddada aniyar rundunar wajen tabbatar da tsaron al’umma, sannan ya yi ƙira ga mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ba su aminta da shi ba ga lambobin kar-ta-kwana na rundunar: 08032003913, 08061581938, 07057337653, da 08028940883; 09022222352.

Leave a Reply