No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Maryam Umar Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta cafke wasu mutane uku da ake zargi Augustine Ikponmwoba mai shekaru 62 da Roland Ibizugbe mai shekaru 63 da kuma Blessing Joseph mai shekaru 36 bisa zargin satar motoci biyu a yayin wani taron ibada coci.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin tare da wasu da ake zargi da aikata laifuka, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP, Funsho Adeboye, ya ce an kama su ne bayan bin diddigin wayar da aka sace tare da motocin da ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya baiwa budurwarsa, Blessing Joseph, a matsayin kyauta.

CP ya ce Misis Joy Mordi da Mista Peter E. Abiwo sun kai wa ‘yan sanda rahoton cewa sun ajiye motocinsu a filin tunawa na Garrick don halartar wani ibadar coci, kuma bayan da suka gama ibada sun gano cewa an sace motocinsu.

KU KUMA KARANTA:‘Ba ‘yansanda ba ne suka kuɓutar da ‘ya’yanmu, biyan kuɗin fansa muka yi’ – Iyayen Nabeeha

A lokacin bincike, an kama matar da ake zargin, Blessing Joseph, wacce ke riƙe da wayar da aka bari a motar Mordi.

Adeboye ya ci gaba da cewa Blessing ta amsa cewa abokinta mai suna Augustine Ikponmwoba ne ya ba ta wayar.

“Kamen Ikponmwoba ya kai ‘yan sanda zuwa Roland Ibizugbe wanda shi ma aka kama. Waɗanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikata kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.”

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...