An Kama barayin katin zaɓe 158 a Kano

1
510

Daga Shafaatu Dauda,kano

Hukumar zaɓe ta ƙasa reshan jihar Kano ta bayyana cewa wasu matasa sun farwa ma’aikatan ta a yankin ƙaramar hukumar Rimingado har suka ƙwace katinan zabe guda 158.

Kakakin hukumar a Kano Ahmad Adam Maulud ne yabbaya hakan.
ya ce ‘’ yanzu haka matasan suna hannun jami’an yan sandan jahar Kano domin gudanar da bincike akan lamarin.

KU KUMA KARANTA:‘Yan siyasa na sayen katin zaɓe -INEC

Matasan da ake zargi sun hada Abduljafur mai shekaru 22 da kuma Saifullahi Rabo mai shekaru 23, da ake zargin yaran wani tsohon dan majalissar dokokin jahar Kano ne.

Wakiliyarmu tayi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, amma lamarin ya ci tura .

1 COMMENT

Leave a Reply