Connect with us

Labarai

An kama ɓarayin da ke haurawa gidajen mutane suna sata a Yobe

Published

on

An kama ɓarayin da ke haurawa gidajen mutane suna sata a Yobe

An kama ɓarayin da ke haurawa gidajen mutane suna sata a Yobe

Daga Ibraheem El-Tafseer

Da safiyar ranar Litinin ne, ana tsaka da ruwan sama, aka kama wasu ɓarayi guda uku, waɗanda suka ƙware wajen haurawa gidajen mutane suna sace musu kayayyaki.

An kama su ne a unguwar Jaji da ke garin Potiskum jihar Yobe, a cikin wani sabon asibiti da ake ginawa, wanda ba a kammala ba.

An same su sun cire dukkan kan famfunan asibitin. Suna tsaka da cire-ciren, dubunsu ta cika aka kama su. Mutanen unguwar ne suka kama su, sannan suka miƙa su ga jami’an tsaron NSCDC da ke Potiskum.

Neptune Prime Hausa ta ziyarci ofishin NSCDC ɗin da ke gundumar Jigawar-Potiskum, kuma ta samu 2IC da ke wajen, Salisu Madu, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce “ba zan yi magana da ‘yan jarida ba, saboda muna kan bincike akan su yanzu haka. Da zarar mun kammala bincike, PPRO ne ke da hurumin magana da ‘yan jarida”

KU KUMA KARANTA: An Kama barayin katin zaɓe 158 a Kano

Wakilinmu ya zanta da ɗaya daga cikin ɓarayin, ga abin da ya ce “suna na Munkaila Isyaka, ni ɗan unguwar Nahuta ne, shekaru na 17.

Da ni makanike ne, daga baya na koma sata. Ba zan iya irga adadin gidajen da na shiga na yi sata ba.

Mu uku muke tafiya, mutum ɗaya zai tsaya a waje, yana gane mana masu wucewa. Mu biyu kuma sai mu shiga cikin gidan.

Abin da muka fi sata shi ne, muna cire duk wani ƙarfe da muka gani a gida, sannan muna zare wayoyin lantarki na cikin gini” inji shi

Ya zuwa haɗa wannan rahoton ɓarayin su uku duka an kama su, suna hanun jami’an tsaron NSCDC ana ci gaba da yi musu bincike, don a gurfanar da su a gaban kotu.

Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Labarai

Matar da ta fi tsufa a duniya ta rasu

Published

on

Matar da ta fi tsufa a duniya ta rasu

Matar da ta fi tsufa a duniya ta rasu

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya, ‘yar kasar Spain, Maria Branyas Morera, wacce aka haifa a Amurka kuma ta ga ‘yan duniya biyu, ta mutu tana da shekaru 117, in ji danginta.

“Maria Branyas ta bar mu. Ta mutu kamar yadda ta yi fata: wato a lokacin da take barcinta, cikin kwanciyar hankali kuma ba tare da jin raɗaɗi ba,” kamar yadda danginta suka rubuta a shafinta na X a ranar Talata.

“Za mu riƙa tunawa da ita saboda nasiharta da kyautatawarta,” in ji su.

KU KUMA KARANTA: Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Issa Hayatou, ya rasu

Branyas, wacce ta rayu tsawon shekaru 20 da suka gabata a gidan kula da tsofaffi na Santa Maria del Tura da ke garin Olot a arewa maso gabashin Spain, ta yi gargadi a cikin sakon da ta wallafa cewa tana jin “raunana”.

“Lokacina ya kusa. Kada ku yi kuka, ba na son a zubar min hawaye. Kuma kar ku wahalar da ni. Duk inda na je, zan yi farin ciki,” ta faɗa a shafin nata wanda iyalanta ke kula da shi.

Guinness World Records a hukumance ya amince da matsayin Branyas a matsayin wadda ta fi kowa tsufa a duniya a cikin watan Janairun 2023 bayan mutuwar Bafaranshe Lucile Randon mai shekara 118.

Bayan mutuwar Branyas, mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya shi ne Tomiko Itooka dan kasar Japan, wanda aka haife shi a ranar 23 ga Mayun 1908 kuma yana da shekaru 116 a duniya, a cewar ƙungiyar bincike kan tsofaffi ta Amurka.

Maria Branyas Morera ta ce tsawon rayuwar da ta samu yana da alaƙa ne da rashin ɗaukar rayuwa da zafi da kula da lafiyar ƙwaƙwalwarta da ta jiki da kuma yin alaƙa mai kyau da mutane.

A yanzu bayan mutuwar Branyas, wani ɗan Japan Tomiko Itooka mai shekara 116 ne zai zama mutum mafi tsufa a duniya.

Continue Reading

Labarai

Za mu shiga yajin aiki matuƙar wani abu ya sami shugabanmu – NLC

Published

on

Za mu shiga yajin aiki matuƙar wani abu ya sami shugabanmu - NLC

Za mu shiga yajin aiki matuƙar wani abu ya sami shugabanmu – NLC

Daga Idris Umar, Zariya

Shugabancin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta yi barazanar yin watsi da duk wasu kayan aiki a duk faɗin ƙasar idan rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tsare shugabanta, Comrade Joe Ajaero.

Kungiyar ta yi wannan barazanar ne a safiyar ranar talata a hedkwatarta, jim kaɗan bayan gudanar da taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta ƙasa, domin tattaunawa kan gayyatar da ‘yan sanda suka yi wa Shugaban NLC, kan zargin tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Hukumar ta NEC ta yanke shawarar cewa Ajaero ya mutunta gayyatar da ‘yan sanda suka yi masa amma ya lura cewa mai ba su shawara kan harkokin shari’a ya nemi ƙarin lokaci domin Shugaban NLC ya gurfana gaban hukumar ‘yan sanda.

Kwamared Ado Kabiru Sani, mataimakin shugaban ƙungiyar NLC, ya buƙaci ma’aikatan ƙasar nan da su kasance cikin shirin ko ta kwana domin samun ƙarin umarni idan ‘yan sanda suka yi abin da ya saba tsammanin tsare Ajaero.

KU KUMA KARANTA: Zanga-Zanga: DSS ta musanta kai samame ofishin NLC

A cewarsa “A matsayinmu na cibiyar ƙwadago, za mu mutunta gayyatar da ‘yan sanda suka yi mana, domin mu ba ƙungiyar da ba ta da fuska ba ce, amma muna aiki da lauyanmu na tsawon lokaci.

“Idan aka kama shugaban mu na ƙasa, duk ma’aikata za su sauƙe kayan aiki nan take.  Ya kamata mu jira ƙarin umarni daga shugabanninmu.”

Continue Reading

Labarai

Mata da miji sun damfari al’umma sama da miliyan 80 a Kano

Published

on

Mata da miji sun damfari al'umma sama da miliyan 80 a Kano

Mata da miji sun damfari al’umma sama da miliyan 80 a Kano

Wasu mata da miji da suka zo garin Bebeji a jihar Kano, suka kama gidan haya suka zauna, mijin ya nemi aikin kamfani a garin sun kai kusan shekara uku, sai suka fara sai da taliya.

A hankali ana zuwa ana saya akan farashi mai sauƙi har ta kai ga mutane ba sa iya sayan taliya a wani gurin sai wajensu, suna sayar da taliya duk guda ɗaya akan naira 600 in kuma a shago ne zaka saya nai ɗari 750 ko sama da haka.

Wannan sauƙin ne ya sa mutane suke tururuwa har da daga wasu garuruwa ana zuwa saya ko mota ɗaya aka kawo a nan take yake ƙarewa.

A hakan wasu ma ba sa samu, sai mutane suka koma ba da kuɗi kafin a kawo taliyan.

Za a ɗauki sunanka idan an kawo duk wanda ya ba da kuɗi ana ƙiran suna a ƙarshe dai ta kai ta kawo tun kafin a kawo za ka ba da kuɗin ka in an kawo sai a ba ka, akwai masu ba da miliyan 4, 5, da dai masu dubun nan ɗarurruka.

KU KUMA KARANTA: Makaho ya damfari wata mata naira miliyan 19, ya yi lalata da ‘yarta da jikarta

A yanzu haka wannan mata da mijinta jiya sun gudu anne mesu an rasa. Sun tafi da kuɗin da ana zaton sun fi million 80.

Muna ƙira ga Jama’a sai a kula ka da wasu su zo garinku da irin wannan dan indai haka suke yi tabbas za su iya zuwa wani garin, sai an saba dasu daga ƙarshe su damfari mutane su gudu. Ubangiji Allah ya kiyaye.

Majiya Tsumagiya ta Kwafoshi

Continue Reading

You May Like