An hukunta korarren sufeton ɗan sanda da ke satar makamai yana sayar wa ƴan bindiga

0
214

Kotun Majistare ta Minna ta yanke wa wani korarren Sufeto na ƴan sanda mai suna Yahaya Mohammed hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin sata da sayar da Magazin na Ak 47 da harsashi ga wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a jihar.

Kafin a kore shi Mohammed, shi ne na biyu mai kula da ɗakin ajiye makamai a hedikwatar ‘yan sandan jihar Neja. Jaridar Vanguard ta wallafa.

An ce ya haɗa baki ne da Ndaman Gana wanda kuma jami’i ne mai kula da sashin kula da makamai na rundunar ‘yan sandan jihar domin aiwatar da wannan mugunyar aikin.

An gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka shafi haɗa baki da kuma satar Magazin na Ak47 da kuma cinikin haramtacciyar magazine ta Ak47 da harsashi.

KU KUMA KARANTA: An kama korarren jami’in tsaro yana ƙoƙarin satar taransifoma

Rahoton ‘yan sanda na farko da aka gabatar a kotu ya bayyana cewa, wasu sahihan bayanai da aka samu daga wata majiya mai tushe daga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ke ƙaramar hukumar Rafi, Kagara, jihar Neja ta bayyana cewa  wani mutum zai yi jigilar kaya a cikin ‘Ghana must go’ wanda ake zargin makamai ne zuwa tashar mota ta Kagara. 

“Sakamakon haka Jami’an ‘yan sanda sun ɗauki matakin kama ku Sufeto Yahaya Mohammed ɗan sanda wanda a da yake aiki a sashen adana makamai na Rundunar Yan sandan jjhar kuma mai matsayi na biyu a sashen”.

“A yayin binciken ‘yan sanda, kai tsohon sifeton ‘yan sanda ka haɗa baki da Ndaman Gana jami’in kula da makamai na ƴan sandan jihar da ke aiki a sashin Operation OPs Minna, kuma ku biyun kun sace magazin 22 da alburusai 61 na rundunar ‘yan sandan jihar Neja. 

“Ku biyun ku sayar da kowace magazin akan kuɗi N1000 kowacce harsashi an sayar da ita akan kuɗi N650 ga wani kofur Sani Mohammed wanda a da yake aiki a Mopol 12 Minna,” in ji rahoton na farko.

Lokacin da shugabar kotun Majistare Hajiya Fati Umar Hassan ta karanta masa tuhumar, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Daga karshe Kotu ta yanke wa Yahaya Mohammed ɗaurin shekara biyu a gidan Yari ko ya biya tarar naira dubu dai (N100,000).

Leave a Reply