An halaka direba da sace mutum 2 a hanyar Abuja

0
299

Wasu ’yan bindiga sun harbe wani direba mai suna Ɗanladi Jobe sun kuma sace kuɗi naira miliyan ɗaya sannan suka yi awon gaba da wasu mutane biyu a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Yahuza Alhassan, wani mazaunin Jere ne da ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho ga wakilinmu a ranar Litinin.

Ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:33 na daren ranar Lahadi a kauyen Dogon-Fili da ke makwabtaka da garin Jere.

Yahuza ya ce, direban yana dawowa ne daga kasuwar ƙauye da ke yankin da ya kai barkono.

A cikin motar da ’yan bindar suka bude wa wuta akwai mai barkonon da wasu fasinjoji da suka ci kasuwa a ranar.

An dai tabbatar da cewa ’yan bindigar sun fito daga daji ne suka bude wa motar wuta, nan take suka kashe direban, suka kuma kwaci miliyan guda daga hanun fasinjojin motar daga bisani suka yi awon gaba da biyu daga cikinsu.

“Bayan sun kashe direban,  sun karbi kudi Naira 980,000 a wurin wani mutum, kafin daga baya su tafi da mutumin da suka karbe wa kuɗi da kuma wani mutum cikin daji,”

KU KUMA KARANTA: Masu tayar da ƙayar baya sun sace sama da mutum 110 a Mali

Wakilinmu ya gano cewa makamancin hakan ya faru a makon da ya gabata, inda wasu ’yan bindiga suka bude wuta kan wata motar bas a kusa da Gadar Malam Mamman.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan bai ɗauki ƙiranmu ba, bai kuma amsa sakon tes da aka aike masa ba game da lamarin har zuwa lokacin da aka kammala rahoton.

Leave a Reply