Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

An gurfanar da wasu ma’aikatan gida biyu a kotu bisa zargin sata

Wata kotun shari’ar Musulunci a Kano a ranar Larabar da ta gabata ta bayar da umarnin a tsare wasu ma’aikatan gida biyu a gidan gyaran hali bisa zarginsu da satar kayan ado da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 1.4 mallakin mai gidan da suke yiwa aiki.

Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Ketura Danjuma, 19 da Aisha Abdullahi, 18, da laifin haɗa baki da kuma sata. Alƙalin kotun, Nura Yusuf-Ahmad, wanda ya bayar da umarnin ɗage ci gaba da sauraren ƙarar zuwa ranar 10 ga watan Mayu.

KU KUMA KARANTA: Shekaru 13 da aure, kotu ta raba su, saboda barazana ga rayuwar ta

Tun da farko, Lauyan masu shigar da ƙara, Aliyu Abideen, ya shaida wa kotun cewa Malam Khalid Mahmoud na Badawa Layout Kano ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Badawa a ranar 30 ga watan Maris.

Ya yi zargin cewa waɗanda ake tuhumar a cikin watan Janairu, sun sace sarƙar zinare na kunnen uwargidan gidan da suke yiwa aiki da ke Layout Badawa a Kano.

Sai dai waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin. Laifin a cewarsa ya saɓawa tanadin sashe na 120 da 133 na dokar shari’ar jihar Kano ta 2000 da aka gyara.


Comments

One response to “An gurfanar da wasu ma’aikatan gida biyu a kotu bisa zargin sata”

  1. […] KU KUMA KARANTA: An gurfanar da wasu ma’aikatan gida biyu a kotu bisa zargin sata […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *