An gurfanar da shi a gaban kotu, saboda cizon leɓen matarsa

0
363
Ta kama mijinta yana lalata da ’ya’yan cikinsu

Wani magidanci mai shekaru 40, Ayodeji Abayomi, ya gurfana a ranar Alhamis a wata kotun Majistire ta Iyaganku, Ibadan bisa zarginsa da cizon leɓan matarsa.

‘Yan sanda sun tuhumi Mista Abayomi, wanda ba a ba da adireshin gidansa da laifin cin zarafi. Ɗan sanda mai shigar da ƙara, Philip Amusan, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Afrilu da misalin ƙarfe 7 na safe a unguwar Abebi, Ibadan.

KU KUMA KARANTA: An maka magini a kotu, bisa laifin satar buhunan siminti 50

Mista Amusan ya yi zargin cewa Abayomi ya cizi leɓan matarsa ​​Lilian na ƙasa. Ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 335 na dokokin aikata laifuka na jihar Oyo, 2000. Mista Abayomi, ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Alƙalin kotun, O. A. Akande, ya shigar da ƙarar wanda ake tuhumar da bayar da belinsa a kan kuɗi naira 50,000 tare da mutane biyu masu tsaya masa.

Ta ɗage sauraron ƙarar har sai ranar 5 ga watan Yuni domin sauraren ƙarar.

Leave a Reply