An gurfanar da matar da ake zargi da kashe abokin kasuwancin ta a gaban kotun majastiri a Kano

0
141

An tuhumi Hafsa Surajo da zargin laifin yunkurin kashe kai da kisan kai wanda ya saɓawa sashi na 281 da 221 na kundin laifuffukan na ƙasa a gaban kotun majastiri mai lamba 37 da ke yan kaba.

Neptune Hausa ta rawaito cewa, Hafsah Surajo da take hannun ‘yan Sanda tace tayi yunƙurin yanka kanta da wuka a gidanta dake unguwa uku inda Na’fi’u wanda yaron gidanta yayi ƙoƙarin hanata inda ta cakamasa a kirji da sassan jikinsa.

Bayan karanta mata tuhumar ta amsa yunƙurin kashe kanta amma ta musanta kashe Na’fi’u.

Mai gabatar da ƙara barista Lamido Abba Soron Dinkin yayi roƙo ƙarƙashin sashi na 295 ACJL da ajiye ta a gidan gyaran halin da tarbiyya kafin a sami shawarwari daga ma’aikatar Shari’a tun da kotun bata da hurumi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sandan jihar Kano sun kama matar da ake zargi da kashe wani mutum (Bidiyo)

Mai Shari’a Hadiza Abdurrahaman ta aike da ita zuwa gidan gyaran halin da tarbiyya sai ranar 1 ga watan 2 na shekara mai kamawa 2024.

Barista Rabi’u Sidi shine lauyan dake kare Hafsan a gaban Kotun.

Leave a Reply