An gano gawar wani mutum wanda ba a san ko waye ba a ƙone a Birnin Kebbi

0
178

An gano gawar wani mutum da ba a san ko waye ba an ƙona shi a shiyyar Takita da ke bayan unguwan Oando a garin Birnin kebbi. Hukumar Hisbah ta jihar Kebbi ta sanar da haka ranar Laraba 20/12/2023.

Hukumar ta wallafa cewa:

ANGA GAWAR WANI MUTUN ƘONANNA WANDA  BA A SAN KO WANENE BA SHIYAR TAKITA BAYAN OANDO GARIN BIRNIN KEBBI”

Ansamu rahoton cewar an kashe wani mutun kuma an ƙonashi a takita bayan oando garin Birnin Kebbi 

Ana sa ran ankashe shi fiye da kwana biyu da suka gabata Amma ba a sanar da hukuma ba sai yau laraba 20/12/2023 bayan jikin sa ya lalace  kawo yanzu baa iya tantance sanadiyar mutuwar wannan bawan Allah 

Bincike yana kan gudana don gano musabbabin wannan ɗayen aikin”

Leave a Reply