An ci Trump tarar dala miliyan 354.9 a New York

A wani hukuncin da ake ganin ya na iya lahani ga harkokin kasuwancin tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, an ci shi tarar kuɗi mai yawa a birnin New York ba ya ga takunkumin kasuwanci da aka ƙaƙaba ma shi.
Ranar Jumma’a, wani alƙali a New York, ya zartas da hukunci cewa, dole tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ya biya tarar dala miliyan ɗari uku da hamsin da huɗu, da dubu ɗari tara (354.9), wanda hakan wani koma baya ne ga tsohon Shugaban na Amurka, wanda wannan shari’a ke barazana ga harkarsa ta gine-gine.

Baya ga tarar, an kuma dakatar da shi daga duk wata harkar kasuwanci a New York na tsawon shekaru uku.

Alƙali Arthur Engoron ya kuma haramta ma Trump zama wani jami’i ko darakta, na kowane irin kamfani ne a New York, na tsawon shekaru uku.

KU KUMA KARANTA:Taron ƙungiyar AU na nemo hanyar warware matsalolin da ke addabar nahiyar Afirka

A ƙarar, wadda Attoni Janar ta New York Letitia James ta gabatar, an tuhumi kamfanonin Trump da iyalinsa da laifin sharara ƙarya wajen bayyana dukiyarsu, da ƙarin dala biliyan 3.6 a shekara guda har na tsawon shekaru 10 saboda su yaudari bankuna su ba su basuka bisa sharuɗɗan masu sauƙi.

Lauyar da ke kare Trump, Alina Habba, ta ce, “Wannan ba kan Trump kawai zai tsaya ba muddun aka bar wannan hukuncin a haka, zai zama wata alama ga kowane Ba’amurke cewa birnin New York ya daina zama wurin kasuwanci.” Ta ce za su daukaka kara.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *