An ceto ɗaya daga ɗaliban jami’ar da aka sace a Katsina

0
191

’Yan sanda sun ceto ɗaya daga cikin ɗalibai mata biyar da aka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma da ke jihar Katsina.

An yi nasarar ceto ɗalibar ce bayan wani samame da Rundunar ’yan sandan ta kai a ranar Litinin.

A cewar kakakin rundunar, ASP Abubakar Aliyu, an ceto ɗalibar wadda ba a bayyana sunan ta ba saboda dalilai na tsaro ne a ƙauyen Bilbis da ke Jihar Zamfara makwabciyar Jihar Katsina.

KU KUMA KARANTA: ’Yan ta’adda a Katsina sun kashe kwamandan jami’an tsaro

Ya jaddada ƙudirin rundunar na yin amfani da wadatattun kayan aiki don ceto sauran ɗaliban huɗu daga da aka yi garkuwa da su.

“Yayin da wadda aka ceto ke samun kulawar likita, Kwamishinan ’Yan sanda ya jinjina wa jami’an rundunar, ya kuma buƙaci jama’a su riƙa taimakawa da bayanai masu muhimmanci don inganta tsaro,” in ji sanarwar.

A ranar 4 ga watan Nuwamba, 2023, mahara suka sace ɗalibai mata biyar a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, inda daga bisani ’yan sanda suka tabbatar da kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da sace ɗaliban.

An sace ɗaliban ne a gidansu da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri Memorial International daura da hanyar Tsaskiya.

Leave a Reply