An cafke ƙasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi yankin Abuja

0
191

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar ‘yansanda a babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da cafke wani mai suna Chinaza Phillip da ya yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane a Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda aka kama Phillip a Kaduna yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jihar Kano tare da yaran sa da kuma waɗanda ya yi garkuwa da su a ranar Alhamis.

An yi musayar wuta mai zafi tsakanin yaran Phillip da ‘yansanda, lamarin da ya kai ga ceto Segun Akinyemi, wani mazaunin Abuja, wanda aka yi garkuwa da shi a lokacin da yake tuƙi bayan ya baro gidansa a ranar Laraba.

Masu garkuwa da mutanen na ɗauke da Akinyemi ne daga Abuja zuwa jihar Kano a lokacin da ‘yansanda suka yi awon gaba da su, kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na ‘yansandan Kaduna, ASP Mansir Hassan ya bayyana.

KU KUMA KARANTA: An kama matashin da ya sace wa mai sana’ar POS dubu ɗari tara a Jigawa

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sanar da kame wasu masu ba da bayanan sirri ga masu garkuwa da mutane.

Wike ya bayyana haka ne a yayin wani taro da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da mazauna garin Gwagwalada da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada ta yankin.

Ya sha alwashin bin diddigin masu garkuwa da mutanen da masu ba su bayanan sirri.

Leave a Reply