An ƙaddamar da shiri kan take haƙƙin yara a Najeriya

0
238
An ƙaddamar da shiri kan take haƙƙin yara a Najeriya

An ƙaddamar da shiri kan take haƙƙin yara a Najeriya

Daga Idris Umar, Zariya

A ranar 8/5/2025 Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen kaddamar da Shirin Aikin Ƙasa na Ƙarshen Ƙeta da Take Hakkin Ƴara a Najeriya, wanda ya kasance babban abin da ya dauki hankali a taron farko na yankin Afirka na ƙasashen Africa Pathfinder Countries karkashin haɗin gwiwar Global Alliance on Ending Violence Against Children.

An gudanar da wannan taro ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ƙasashe da dama suka tattauna hanyoyin da za a bi wajen dakile cin zarafi da kuma kare rayuwar yara a nahiyar Afirka.

A jawabinsa, Shettima ya jaddada bukatar aiwatar da dokar kare hakkin yara (Child Rights Act) da sauran dokoki da ke tabbatar da tsaron lafiyar yara, mutuncinsu da kuma kyakkyawar makomarsu. Ya ce lokaci ya yi da za a mayar da hankali wajen tabbatar da cewa dokokin kare yara sun samu karbuwa a matakin kasa da jihohi.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana wasu matakai na ainihi da gwamnatin Tinubu ke dauka don inganta kariyar yara a fadin ƙasar. Ciki har da:

KU KUMA KARANTA: Mataimakin shugaban Najeriya ya buɗe taron gwamnonin yankin tafkin Chadi

Kafa Hukumar Kare da Raya Ƙarfin Yara ta Ƙasa (National Child Protection and Development Agency) wadda za ta mayar da hankali kan tsaron lafiyar yara da inganta rayuwarsu;

Kaddamar da Tallafin Ƴara Na Ƙasa (Universal Child Grant) domin rage talauci a cikin gidaje da kuma taimaka wa yara marasa galihu;


Kafa sa Bayanan Tsaro da Walwalar Yara ta Ƙasa (National Child Protection Database) da kuma Alƙaluman Jin Daɗin Rayuwar Yara (Child Well-being Index) domin auna ci gaban da gwamnati ke samu da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Shettima ya ƙara da cewa, idan ana son samun nagartaccen ci gaba a harkar kare yara, sai an hada hannu da hukumomin tsaro, al’umma da kuma kungiyoyin farar hula wajen tabbatar da cewa yara sun samu kariya daga duk wani nau’in barazana.

Taron ya kara fayyace matsayin Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan ƙasashen nahiyar da ke ƙoƙarin tabbatar da Ƙarshen Cin Zarafin Ƴara.

Leave a Reply