An ƙone gidan mawaƙi Rarara Kano

0
381

Daga Shafaatu DAUDA, Kano

Rahotanni na cewa wasu gungun matasa sun ƙone gidan mawaƙi Dauda Kahutu Rarara dake unguwar Zoo road a Kano.

Wannan ya biyo bayan sanar da sakamakon zaɓen gwamna da aka yi da safiyar yau litinin a birnin Kano, wanda ɗan takara a inuwar jam’iyar NNPP Eng. Abba Kabir Yusuf ya lashe.

KU KUMA KARANTA: An sanya dokar hana fita a Kano

Rarara shahararren mawaƙin siyasa ne musamman ma a arewcin Nijeriya, kuma a yammacin jiya lahadi ya saki wata sabuwar waƙa inda yake cewa Gawuna ya kayar da Abba.

Dauda Rarara ya koma yi wa jam’iyar APC waƙa tun a shekarar 2015 zuwa yanzu , wanda ke yin zamɓo da habaici cikin waƙoƙinsa.Wanda hakan ke baƙanta ran magoya bayan waɗanda aka yi wa zambon.

Leave a Reply