Amurka ta gargaɗi Isra’ila kan shirin kai wa Iran hari

0
107

Amurka ta yi gargaɗin cewa idan Isra’ila ta zaɓi ɗaukar fansa ta hanyar soji kan harin ramuwar gayya da Iran ta kai mata, to Amurka ba za ta taimaka mata ba.

Gwamnatin Amurka ta yi wannan gargaɗi ne a yayin da Isra’ila ke tunanin kai hari a matsayin martani kan harin ramuwar gayya da Iran ta kai mata a ƙarshen mako.

Gwamnatin Biden ta bayyana karara cewa Amurka ba za ta sa hannu a hare-haren soji da Isra’ila ke tunanin kaiwa Iran ba, saboda fargabar ɓarkewar yaƙi a Gabas ta Tsakiya.

Wani babban jami’in ƙasar ya shaida wa ’yan jarida jim kaɗan bayan kawo karshen harin na Iran cewa “Mun yi imanin Isra’ila na da ’yancin ta kare kanta.”

Amma da aka tambaye shi ko Amurka za ta taimaka wa Isra’ila wajen tunkarar hare-haren soji, sai kaiwa ko, sai jami’in ya ce a’a, “Ba ba tunanin sanya kanmu cikin irin wannan abu.”

A cewar wani jami’in kuma, Amurka ta riga ta isar da wannan sakon kai tsaye ga manyan jami’an Isra’ila a lokacin wata ganawar sirri ta wayar tarho ranar Lahadi tsakanin Sakataren Tsaro Lloyd Austin da Ministan Tsarnn Isra’ila Yoav Gallant.

KU KUMA KARANTA: Wasu ‘yan Nijar sun yi zanga-zangar neman ficewar sojojin Amurka daga ƙasar

Jami’in ya ce Austin ya bayyana ƙarara cewa Amurka ba ta shirin shiga wani hari da za a iya kaiwa a madadin Isra’ila.

Wannan dai wani mataki ne da ba a saba gani Amurka ta dauka kan kawar tata ta kut-da-kut ba, wadda ta shafe gomman shekaru tana samun kariya da taimakon sojin Amurka fiye da kowace ƙasa a duniya.

Wannan dai na zuwa ne bayan Isra’ila ta kwashe watanni tana yin gaban kanta a kan Falasɗinawa a yankin Zirin Gaza — duk da irin kakkausar suka da take sha daga Amurka da sauran kawayenta cewa matakan sojin sun wuce gona da iri.

Harin da Iran ta kai kan Isra’ila da yammacin ranar Asabar ya yi matukar kidima shugabannin duniya, ciki har da jami’an Amurka.

Fadar White House ta ce da farko sun dauka cewa Iran na shirin harba wa Isra’ila makamai masu linzami kadan ne kawai.

Wani babban jami’in Amurka ya bayyana cewa sun kadu a yayin da suka samu bayanai cewa jami’an leken asirin Amurka sun yi imanin cewa Iran na shirya harba makamai masu linzami fiye da 100 ka Isra’ila.

An dauki harin a matsayin ramuwar gayya ga harin da aka kai wani wuri da Iran ta kira karamin ofishin jakadancinta da ke birnin Damascus na kasar Syria, wanda ake kyautata zaton Isra’ila ce ta kai harin.

A halin da ake ciki kuma, akalla makamai masu linzami na Iran guda tara ne suka yi barna a cikin Isra’ila, biyu daga cikinsu a sansanonin sojin saman gwamnatin Isra’ila.

Wani babban jami’in Amurka ya shaida wa ABC News cewa makamai masu linzami guda biyar na Iran kuma sun afka wa tashar jirgin soji Nevatim Air Base, inda suka lalata wani jirgin jigilar soji kirar C-130.

Ya ƙara da cewa wasu karin makamai masu linzami hudu sun afka wa sansanin sojin saman Negev, amma ya ce babu wani rahoto na “gaggarumin ɓarna” da suka yi.

Leave a Reply