Amurka da Rasha sun yi maraba da yarjejeniyar musayar fursunonin yaƙi ta Isra’ila da Hamas

0
181

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa ya ji daɗi matuƙa kan cewa za a saki wasu daga cikin waɗanda Hamas ke rike da su a ƙarƙashin yarjejeniyar da aka cimmawa.

Mista Biden ɗin ya bayyana cewa an saki Amurkawa biyu waɗanda aka kama a ƙarshen watan Oktoba bayan an yi tattaunawa ta diflomasiyya mai zurfi.

KU KUMA KARANTA: Rundunar Sojin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar sakin fursunonin yaƙi, da tsagaita wuta na wucin-gadi da Hamas

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa ƙasarta na maraba da wannan yarjejeniya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na RIA na ƙasar ya ruwaito.

Leave a Reply