Amfanin yalo da muhimmancinsa ga lafiyar jikin ɗan adam

0
298

Bincike da dama da masana suka gudanar ya nuna cewa yalo ya samo asali ne daga ƙasashen Indiya da kuma Afirka, amma kuma yanzu ana noma shi a faɗin duniya.

A Najeriya an fi noma yalon ne a yankin arewacin ƙasar inda akan kuma same shi a kasuwanni daban-daban a faɗin ƙasar.

Za a iya cin ɗanyensa wanda wasu sukan haɗa da soyayyar gyaɗa ko su riƙa dangwalawa a haɗaɗɗen garin yaji ko kuma soyayyiyar miya su riƙa ci.

Ɗaya daga cikin abubuwan ban mamaki game da yalo shi ne yana fitowa a nau’uka daban-daban, wanda ya danganta da yanayi da kuma wurin da ake noma wa.

Yana kuma fitowa a launuka da kuma fasali da girma da kuma ɗanɗano daban-daban. Akan samu masu launukan fari, da ruwan goro, da kore, da algashi da dai wasu launuka.

A kudancin jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya akwai ƙabilar Baburawa da kan yi amfani da gauta wato ɗaya daga cikin nau’in na yalo wajen abinci, su kan riƙa haɗawa da tuwo suna gutsura suna ci.

Malama Adama Hassan wacce ‘yar ƙabilar Babur ɗin ce da ke zaune a garin Biu na jihar Borno inda Baburawan suka fi yawa, ta shaida wa BBC cewa suna matuƙar muhimmantar da Yalo ko ɗata, ko kuma gauta a matsayin cimaka.

”A ko da yaushe ba za ka taɓa rasa gidan Baburawa da gauta ko yalo ba, saboda muna haɗa shi da abinci, musamman tuwo, yana a matsayin miya ne, mu kan riƙa gutsurar shi mu haɗa da tuwo muna ci.”

Amfanin yalo ga lafiyar jikin ɗan adam

KU KUMA KARANTA: Ko ka san amfanin ƙwallon Mangwaro a jikin mutum?

Galibin mutane na cin Yalo ne kawai don nishaɗi ko kashe yunwa ba tare da fahimtar irin ɗimbin amfanin da yake da shi a jikinsu ba.

A nan za mu duba amfanin yalo da kuma muhimmancin sa a jikinmu. Ba zai yiwu mu kawo duka ba, to amma za mu tsakuro kaɗan daga cikin amfaninsa:

Kamar yadda mujallar kiwon lafiya ta Medical News Today da ke Amurka ta wallafa, binciken da masana da dama suka gudanar game da yalon ya nuna cewa yana da matuƙar amfani ga lafiyar jikin ɗan adam kamar yadda ‘ya’yan itace suke da shi.

Jerin wasu daga cikin amfanin yalon

  1. Rage ƙiba

Kamar yadda Misis Megan Ware wata ƙwararriya a fannin abinci mai gina jiki a Amurka kuma manomiyar kayan lambu ta wallafa a mujallar Medical News Today, yalo na da matuƙar amfani wajen rage ƙiba saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke taimaka wa ƙona kitsen jikin mutum wanda kan sa a rage ƙibar.

Malama Husna Abubakar wacce ke zaune a garin Abuja babban birnin Najeriya ta shaida wa BBC cewa maigidanta wanda ke da ƙiba sosai ba ya rabuwa da sayen yalo saboda yana da yaƙinin cewa yana da matuƙar amfani wajen rage ƙiba.

”Na ga yana yawan sayen yalo kuma yakan saka ni in yanka masa ƙanana kamar yadda ake yanka su kankana in kawo masa a ko wane dare ya ci kafin ya kwanta,” in ji Husna.

  1. Kare garkuwar jikin ɗan adam

Kamar yadda mujallar Healthline ta Birtaniya ta wallafa a wata mujallar kiwon lafiya, sinadaran Anthocyanins, da nasunin da kuma flavonoids sinadaran kashe ƙwayoyin cuta ne masu ƙarfi da ke ƙunshe cikin yalo da kuma kan taimaka wajen bayar da kariya ga garkuwar jikin ɗan adam tare da ƙara inganta lafiyar jikin.

Sinadarin Anthocyanins na taimaka wa wajen bayar da kariya daga yaɗuwar ƙwayoyin halittar da ke haddasa cutar kansa har ma da sauran cututtukan da ƙwayar cutar bacteria ke haddasawa.

  1. Inganta aikin jijiyoyin jini

Yalo yana ƙunshe da sinadaran vitamin B kamar su thiamin, da niacin, da B6 da kuma pantothenic acid waɗanda ke taimakawa wajen amfani da sinadaran fat da na protein; kana suna bayar da gudumawa mai amfani ga hanyoyin jijiyoyin sadarwar ƙwaƙwalwa.

Sinadarin vitamin B na taka muhimmiyar rawa wajen inganta kiwon lafiya. Yana taimaka wa wajen inganta aikin ƙwaƙwalwa tare da tabbatar da cewa hanyoyin jijiyoyin sadarwar ƙwaƙwalwa da na garkuwar jikin ɗan adam na aiki yadda ya kamata.

  1. Ƙarfi da lafiyar ƙashi

Saboda sinadaran minerals irin su folate, da manganese, da vitamin K, da magnesium, da vitamin da kuma Copper da yalon ke ƙunshe da shi, yana taimaka wa wajen ƙara ƙarfi da lafiyar ƙashi. in ji Mujallar Medical News Today ta Amurka.

Cin yalo a ko da yaushe yana da matuƙar muhimmanci wajen bayar da kariya daga haɗarin lalacewar ƙashi da kuma rashin ƙwarin ƙashi.

  1. Narkar da abinci a jiki

Kamar yadda bayanai suka nuna daga farko, yalo na da sinadarin da ke taimaka wa sosai wajen narkar da abinci a jikin ɗan adam (fibre) tare da taimakawa a yanayin yin bayan gida.

Saboda wannan sinadarin da ya ƙunsa, suna rage yawan kumburin ciki da rashin yin bayan gida sosai ta hanyar inganta narkewar abincin.

Sinadarin na matuƙar taimakawa a lafiyar cikin ɗan adam da kuma motsawar dattin ciki da yin bayan gida cikin sauƙi.

  1. Amfani ga mata masu juna biyu

Wannan cimaka na ƙunshe da sinadaran minerals, da vitamins da kuma sauran abubuwan gina jiki da ke taka muhimmiyar rawa a lokacin da mace ke ɗauke da juna biyu.

Abubuwan da ke ƙunshe cikin yalo na taimaka wa mata masu juna biyu da jariran da ke cikinsu wajen kasasncewa cikin ƙoshin lafiya.

  1. Bayar da kariya daga matsalar ƙarancin jini

Masana sun gano cewa yalo ka iya zama wani magani na warkar da cututtuka kamar na numfashi, da kumburin ciki, da ciwon kai, da sauran su idan ana ci a ko da yaushe.

Yalo kan taimaka wajen ƙara yawan ƙwayoyin halittar jini a jiki, don haka yana yaƙi da matsalolin da ke haddasa ƙarancin jini ko kuma sinadarin iron.

Yana kuma ƙunshe da sinadaran copper, tare da taimakawa wajen inganta ƙara yawan zagayawar ƙwayoyin halittar jini sosai ta hanyar jijiyoyin jinin ɗan adam, don haka yana ƙara ƙarfi da kuzari.

  1. Kariya daga kamuwa da ciwon suga (Diabetes)

Ta ɓangaren ciwon suga ko kuma diabetes kuma, yalo na taimakawa wajen bayar da kariya saboda yana ƙunshe da sinadarin fibre mai saurin narkewa da kuma carbohydrates da kan shi ma kan taimaka.

Nau’ukan abinci masu ƙunshe da fibre da carbohydrates na taimakawa wajen tantance yanayin tsotsewar suga da bulkodin jini.

Abinci ne mai kyau ga masu fama da ciwon suga, saboda yana ragewa tare da bayar da kariya daga kamuwa daga cutar suga ko diabetes mataki na 2.

  1. Daidaita hawan jini (BP) da kitsen cikin jini (cholesterol)

Har ila yau yalo na ƙunshe da sinadarai minerals masu yawa na calcium, da magnesium, da potassium, da kuma phosphorus da ke taimakawa wajen daidaita ayyukan ƙwayoyin halitta da sinadaran jiki a cikin jiki, don haka yana daidaita yanayin adadin ƙarfin zagayawar jini wanda ke bayar da kariya daga cutar hawan jini.

Don haka yawan cin yalo na taimakawa wajen daidata ƙarfin hawa da sauƙar jini da kuma kitsen cikin jinin.

  1. Bayar da kariya daga cututtukan zuciya

Ta ɓangaren cutattukan da ke shafar zuciya kuma, yalo wanda ke ƙunshe da sinadaran vitamin B1 da B6 (thiamine da niacin).

Waɗannan sinadarai na vitamins na da muhimmanci a cikin jiki wajen ayyukan zuciya da kuma fitar da zufar jiki.

Suna kuma ƙunshe da sinadarin potassium da ke taimakawa wajen daidaita ƙarfin aikin jinin jiki.

Gargaɗi da shawarar masana game da cin yalon da ya wuce ƙima
Duk da irin ɗimbin amfanin da aka bayyana cewa yalo na da shi ga lafiyar jikin ɗan adam, akwai kuma gargaɗi da masana ke yi na matsalolin da ka iya faruwa idan aka riƙa cin yalon da ya wuce ƙima.

Don haka yana da kyau idan za a ci yalo a riƙa ci daidai gwargwado don kaucewa matsalolin da ka iya biyo baya cin shi da yawa.

Leave a Reply