Amfanin ‘Dental floss’ a haƙora don tsaftace baki

Daga Aisha Musa Auyo

Dental floss dai wani zare ne siriri na roba da ake sawa a tsakanin haƙora don cire abincin da ya maƙale a wurin. Wannan abinci da ke maƙale a tsakanin haƙora, brush ba ya fitar da shi. Shi ne yake taruwa ya zama ‘plaque’. Shi plaque ɗin wannan abincin da ya maƙale ne yake taruwa sai ya zama abincin bacteria.

Wannan dattin yana sa baki wari, yana sa haƙora su canza kala. Yana sa haƙora su yi ta ciwo wataran ma har sai an cire haƙorin, domin wannan bacteriar da ke ci daga gareshi tana kashe haƙori.

To shi wannan zaren yana zuwa a nau’i daban-daban, an yi shi ne siriri yadda ze iya shiga tsakanin haƙora yana fito da duk abin da ya maƙale ba tare da an wahala ba ko an ji zafi. Wani yakan zo da ƙamshin minti, vanilla, da sauransu, wani kuma kawai zaren ne babu ƙamshi.

Mafi yawancin ciwon haƙori ko warin baki wannan maƙallen abincin ke kawo shi. Idan mutum ya je Asibitin haƙori, akan yi masa wannan sakace tsakanin duk haƙoransa duka. Wato duk ranar da kuka fara flossing zai sha mamakin abin da zai fito tsakanin haƙoranku.

KU KUMA KARANTA: Sama da mutane miliyan 73 ne ke fama cutar ruɓewar haƙora a Filipin

Wato abin ya bani mamaki da na tambayi mutane ko suna flossing na ga da yawansu ba su ma san mene ne shi ba. Kamata ya yi flossing ya zama normal kamar brush. A ƙa’ida akan so mutum ya yi wannan sakacen tsakanin haƙoran kamar sau biyu a rana, yadda yake brush, amma mutum zai iya yin fiye da haka. In da hali duk lokacin da mutum ya ci abinci ya kamata ya yi flossing.

Akwai mouth wash da kan taimaka wajen fitar da waɗannan maƙallalun abincin, yayin da aka kurkure baki da shi na mintuna. Haka zalika, kurkure baki da ruwan kananfari ma na taimakawa wajen fiddasu. Amma babu abin da ya kai saka wannan zare a tsakanin haƙora ɗaya bayan ɗaya fitar da wannan abu da ke maƙalewa a tsakanin haƙoran.

Dan Allah a guji tsinken sakace, ba ɗaya yake da floss ba. Shi tsinken yana da kauri yana sa a samu rami tsakanin haƙoran da ake yawan sakace wa. Sannan katako ne yakan karye ma, kuma yakan jima mutum rauni.

A taƙaice, yin floss na ƙara wa mutum lafiyar haƙora, kyan haƙora, numfashi mai tsafta, da kuma jin daɗi wajen mua’amala da jamaa. Yin floss na raba mutum da ciwon haƙori, da kuma dauɗar haƙora. Floss na da sauƙin kuɗi sosai, ana iya samunsa a manyan shaguna, ko asbitin haƙori, har ma da wurin masu sayar da robobin abincin biki, domin ana sa shi a cikin packs ɗin abinci.

Dan Allah ka da mu yi wasa da yin floss. Akwai Hadisin da Annabi Muhammad (SAW) ya ce, ba dan ka da ya takurawa al’ummarsa ba, da ya mayar da yin aswaki kafin yin kowacce sallah ya zama wajibi. Wannan yana nuna mana tsantsar amfanin tsaftar baki ko a addini ma.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *