Daga Rabo Haladu Da Imrana Mustapha
Allah Ya yi wa babban malamin addinin nan na Kano Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba, wanda aka fi sani da Kala Haddasana rasuwa a yau Juma’a.
Wasu iyalansa ne suka tabbatar wa da manema labarin rasuwar.
Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.
Malamin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya inda ya kwana ɗaya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.I
Iyalansun sanar da cewa anyi jana’izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma’a.
Wani daga cikin ƴaƴansa Abdul ya shaida cewa ya kusan shekara 82, don an haife shi ne a shekarar 1940.
Kala Haddasana kamar yadda aka fi saninsa da shi ɗan asalin ƙasar Ghana ne kuma a can aka haife shi.
“Ya dawo Najeriya ne bayan da ya yi karatun digirinsa a Saudiyya, sai ya koma Najeriya ya fara koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano har ya yi digirin-digirgir.
“Ya koyar a fannin Islamic Studies kuma ya jima yana koyarwar,” a cewar ɗan nasa.
Malamin ya bar yara 28 zuwa 30 kamar yadda ɗan ya shaida mana