Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood Maimuna Musa
Daga Jameel Lawan Yakasai
Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango ya angwance da jaruma Maimuna Musa.
Shugaban hukumar tace fina-finai da ɗab’i na Jihar Kano Abba El-Mustapha ne ya wallafa labarin auren nasu a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Inda yace Adam Zango Allah ya sanya alkhairi yabada zaman lafiya, tare da sanya hoton Ango da Amaryar a shafinnasa na Facebook.
Auren dai ya zo cikin bazata, domin babu wanda ya san da neman sai labari aka ji jaruman sun shiga daga ciki.
KU KUMA KARANTA: Fittaccen jarumin Kannywood Adam A. Zango Yayi Hatsarin mota
Jaruma Maimuna matashiya ce wadda tauraronta ya fara haskawa a Kannywood.
Ta yi fina-finai kamar Kwana Casa’in, Garwashi da sauransu.
A baya-bayan nan ma fitacciyar jaruma a masana’antar, Rahama Sadau, ita ma ta yi aure, lamarin da ya bai wa mutane da dama mamaki.









