Adadin marasa aikin yi ya ƙaru matuƙa a Najeriya – NBS

0
86

Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya, (NBS), ta bayyana cewar, an samu gagarumar ƙaruwa a mizanin rashin aikin yi a Najeriya a zango na 3 na shekarar 2023.

A rahoton wani bincike data gudanar game da yawan ma’aikatan Najeriya a zango na 3 na shekarar 2023 wanda aka wallafa a Litinin ɗin da ta gabata, hukumar NBS ta bayyana cewar mizanin rashin aikin yi a Najeriya ya yi tashin gwauron zabi daga kaso 4.2 cikin 100 a zango na 2 na shekarar 2023 zuwa kaso 5.0 cikin 100 a zango na 3 na shekarar.

A cewar NBS an samu ragowar ma’aikatan da suka shiga cikin bincike tsakanin mutanen da ke da shekarun yin aiki daga kaso 80.4 cikin 100 a zango na zuwa kaso 79. 5 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023.

A sharhin da tayi game da ƙididdiga, NBS tace, mizanin auna yawan masu aikin yi da adadin yawan al’umma ya kasance akan kaso 75.6 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023 inda ya ragu da kaso 1.5% idan aka kwatanta shi dana zango na 2 na wannan shekarar.

“Gamayyar mizanin rashin aikin yi da na ƙarancin guraben aikin yi dake da nasaba da lokaci a matsayin wani kaso na adadin masu aikin yin dake cikin al’umma (lu2) ya karu da kaso 17.3 cikin 100 a zango na 3 na shekarar daga kaso 15.5 cikin 100 na yadda yake a zango na 2 na shekarar.

“Kimanin kaso 87.3 na ma’aikatan da aka gudanar da ƙididdigar akansu a zango na 3 na shekarar 2023 masu sana’ar kansu ne.

“Kason ma’aikatan dake aikin albashi a zango na 3 na shekarar 2023 ya kai kaso 12.7 cikin 100.

Mizanin rashin aikin yin yayi gagarumar karuwa a zango na 3 na shekarar 2023 da kaso 5 cikin 100. An samu karuwar kaso 0.8 cikin 100 daga yadda yake a zango na 2 na shekarar ta 2023.

“Mizanin rashin aikin yin tsakanin mutanen da suka kammala karatun sakandare ya kai kaso 7.8 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023.”

A cewar Hukumar Kididdigar Najeriya ta NBS, mizanin rashin aikin yi tsakanin matasan dake tsakanin shekara 15 zuwa 24 ya kai kaso 8.6 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023, inda aka samu karuwar kaso 1.4 cikin 100 akan yadda al’amarin yake a zango na 2 na shekarar.

Mizanin rashin aikin yin a birane ya kai kaso 6.0 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023, inda aka samu ‘yar karuwa da kaso 0.1 cikin 100 akan yadda yake a zango na 2 na shekarar.

KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar NARTO ta dakatar da yajin aikin gamagari, ta umarci ma’aikatan ta su koma bakin aiki

Kididdigar karancin guraben aikin me nasaba da lokaci ta kasance akan kaso 12.3 cikin 100 a zango na 3 na shekarar 2023, inda aka samu ‘yar karuwa da kaso 0.5 cikin 100 yadda yake a zango na 2 na shekarar. hakan na nuni da samun karuwar kaso 1.4 cikin 100 idan aka kwatanta da yadda yake a zangon na 4 na shekarar 2022.

“Kaso 4.1 cikin 100 na wadanda ke tsakanin shekarun yin aiki duk a harkar noman ci da karfi suke a zango na 3 na shekarar 2023.

Kididdigar mutanen dake aikin da ba na hukuma ba a zango na 3 na shekarar 2023 ya kai kaso 92.3 cikin, yayin da a zango na 3 na shekarar ya kasance akan kaso 92.7 cikin 100.

Rahoton ya kara da cewar, adadin matasan da basa aiki ko karatu ko koyon wata sana’a (neet rate) a zango na 3 na shekarar 2023 ya kai kaso 13.7 cikin 100.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here