Abubakar Cargo ya gina hanyar magudanar ruwa na tsawon kilomita 3 a Potiskum
Alhaji Abubakar Adamu Waziri wanda aka fi sani da Cargo, ya gina hanyar magudanar ruwa na tsawon kilomita 3 a Masaƙar Makafi har zuwa tashar Gawo a cikin garin Potiskum jihar Yobe.
Wannan yanki na unguwar Masaƙar Makafi sun ɗauki tsawon lokaci suna fama da rashin hanyar magudanar ruwa. Duk lokacin da aka yi ruwan sama, to ruwan ya kan mamaye hanyoyin unguwar a rasa hanyar wuce. Amma yanzu Cargo ya gina musu babban kwalbati mai inganci, don sauƙaƙa wa al’ummar yankin.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar Mutane 50 a Jihar Neja
Mazauna yankin da dama sun shaidawa Neptune Prime farin cikinsu kan yadda Abubakar Cargo ya gina musu magudanar ruwa domin kawo musu ƙarshen matsalar hanyar ruwa da suka daɗe suna fama da shi.
Wani mazaunin unguwar mai suna Ahmad Ibrahim ya ce “a baya kafin a yi mana wannan kwalbati, har fargaba muke idan muka ga hadiri za a yi ruwan sama, ba mu da hanyar da ruwan zai wuce, sai dai ya mamaye titin gabaɗaya. Muna matuƙar godiya ga Injiniya Abubakar Adamu Waziri, kuma tabbas za mu rama masa a lokacin zaɓe”.



Alhaji Abubakar Adamu Waziri (Cargo) ya tsaya takarar neman kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Potiskum da Nangere a shekarar 2023, a ƙarƙashin jam’iyar PDP, amma bai yi nasara ba.
Yanzu kuma ya canza sheƙa zuwa sabuwar jam’iyar haɗaka ta ADC, har yanzu ma dai shi ne zai tsaya takarar kujerar neman ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Potiskum da Nangere a zaɓen 2027.










