Ambaliyyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar Mutane 50 a Jihar Neja
Daga Jameel Lawan Yakasai
Rahotanni daga Karamar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja, sun bayyana cewa ambaliyar ruwa mai tsananin karfi ta hallaka mutane da dama tare da lalata gidaje da kadarori na miliyoyin nairori.
Mazauna garin sun ce sakamakon ambaliyar ruwan, hanyar da ke hada shiyyar Arewa da Kudancin Najeriya ta karye.
To sai dai har zuwa yanzu ba a tabbatar da cikakken adadin wadanda suka mutu ba.
KU KUMA KARANTA: Yan Arewa su Shiryawa Ambaliyar Ruwa_ACF
Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa akalla mutane 50 ake zargin sun mutu wadanda yawancinsu mata ne da kananan yara, yayinda har zuwa Lokacin hada wannan rahoto ba akai da gano wasu daga cikin wadanda ruwa ya yi gaba da su ba.
Ambaliyar dai ta faru ne sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi a daren Laraba da ya dauki tsawon lokaci ya na zuba.
Rahotanni sun nuna cewe yadda alummar yankin ke rokon hukumomi da su kai musu daukin gaggawa.