Connect with us

Labarai

Abin da ya sa muka ce za mu rufe kasuwar Potiskum, kuma mu yi zanga-zangar lumana – Shugaban ‘yan kasuwar Potiskum

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

A makon da ya gabata ne, shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan kasuwar Potiskum, Alhaji Nasiru Mato ya fitar da sanarwar cewa za su rufe kasuwannin da suke cikin garin Potiskum, sannan za su gudanar da zanga-zangar lumana. A wannan tattaunawar, Alhaji Nasiru Mato ya bayyana dalilansu na fitar da wannan sanarwa da kuma sauran batutuwa da dama da suka shafi kasuwa da ‘yan kasuwar Potiskum.

Ga yadda hirar ta su ta kasance da wakilinmu Ibraheem El-Tafseer;

NEPTUNE HAUSA: Da farko muna so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu.

ALHAJI NASIRU MATO: Suna na Alhaji Nasiru Mato shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ‘yan kasuwar Potiskum da kewaye.

NEPTUNE HAUSA: Ko mene ne ya faru aka ga shafinku na na ‘yan kasuwar Potiskum (UMAPO) kun fitar da sanarwar za ku fita zanga-zangar lumana, sannan za’a rufe kasuwannin cikin garin Potiskum?

ALHAJI NASIRU MATO: Eh to! Abin da ya sa muka fitar da sanarwar za mu fita mu yi zanga-zanga na lumana, to ba komai ba ne ya sa, sai abin da ya ke faruwa tsakaninmu da ƙaramar hukumar Potiskum. To mu dai mun sani cewa akwai gwamnati na ƙaramar hukuma da jiha da na tarayya duka. Kuma mun san ko’ina akwai shugaba da ya ke shugabantar wannan wuri. Sannan muma a matsayinmu na shugabanni wanda mu ke wakiltar al’umma, kuma ɓangarenmu shi ne ɓangare ma fi rinjaye, ɓangare ma fi al’umma.

Ba ma a Potiskum ba, a ko’ina, duk duniya ma ɓangaren ‘yan kasuwa ya fi kowane ɓangare yawan al’umma. Ba wai mun ce kowane abu ne sai an sanar da mu idan za’a yi ba, amma akwai abin da idan ya shafeku, yana da kyau kafin a yi, a tuntuɓe ku, a ji shawararku. Duba da yanayi da ake ciki, na matsatsi da rashin abin yi. Har Allah ya sa ana iya samun wasu suna iya yin sana’a su da kansu, domin su ciyar da iyalansu, su taimaki wasu mutane, ba su ɗora wa gwamnati nauyi ba. Ba su roƙi kowa ba, ba su zama ‘yan ta’adda ba.

To muna ganin wannan babban abin alfahari ne, ga duk inda shugaba ya ke, idan har ya kasance yana jagorantar irin waɗannan mutane a ƙaramar hukumarsa ko a jiharsa. Zai iya yin alfahari da bugar ƙirji.

To sai muka samu labarin gefen ‘Police Station’ an ba su takarda su ta shi, saboda wani dalili. Sannan sai ofishin ‘Road Safety’ an ba su sati biyu su kwashe kayansu, ana so su tashi, saboda gwamnati za ta gina ‘Plaza’ domin a sayar wa mutane. Ka ga a nan akwai ayar tambaya, gwamnati za ta yi plaza. To plaza ɗin da za ta yi, ita gwamnati ɗin ne za ta zuba kaya a ciki ta dinga sayar wa mutane? Ko kuma ‘yan kasuwar da take kora su bar wajen, take faɗa da su, sune take tsammanin za su saya a su yi kasuwanci a ciki.

Akwai ayar tambaya. Misali ni ne nake so na yi abu na ci gaba don kai, sai nake faɗa da kai ina korarka, to idan na yi abin ni ne zan sake kiranka mu yi sulhu, ka zo ka yi amfani da abin?

Sai na uku, akwai kasuwar NPN. Wadda tana da shekara 34 da yin waɗannan shagunan ‘shopping complex’ ɗin, wanda Alhaji Barde Gadaka ya yi, wanda kuma an bawa ‘yan siyasa manya da ƙanana a wancan lokacin, kuma gwamnatin wancan lokacin ita ta bayar.

Ai gwamnati ba ta fi gwamnati ba, mu abin da muka ɗauka a gwamnati kawai ci gaba ne, idan ka zo za ka ɗora a inda wani ya tsaya ne. ba wai idan ka zo ka ce wane bai iya ba, wancan bai iya ba, kai ne ka fi kowa iyawa. Ƙaramar hukuma ta ce, ya ce ya soke takardar izini na mallakar wannan wuri da aka bawa mutane.
Kenan waccar gwamnatin da ta bayar a baya, ita ba ta iya ba kenan? Sai yace shi ba ruwansa da wadda gwamnatin ta bayar a baya. Shi da wanda yake cikin shago yake Magana a yanzu. Ka ga wannan wata rigima ce wadda za a kunno ta, kuma ba a san ƙarshenta ba. Saboda waɗanda aka bawa shagunan a baya, ‘yan siyasa ne, kuma an basu ne don su ma su samu na cefane a gidajensu.

Ba mu ce gwamnati shagunan nan ba nata bane fa, ba mu ce gwamnati kar ta sabunta takardun shagunan ba fa, amma sai a bi bisa tsari. Ba inda ba a sayar da ‘allocation’ ko na gida ko na kasuwa, ba inda ba a sayar dashi. Idan ma laifi ne, to duk ƙasar nan ana yi, a kowace jiha da ko’ina.

A jihar Yobe muna da ƙananan hukumomi 17, a dukkan waɗannan ƙananan hukumomi babu inda ake irin wannan abun sai a Potiskum kaɗai. A Potiskum kaɗai ake ƙirƙirar irin waɗannan abubuwa.

To wannan shi ne dalilinmu, muka ga cewar tun da ba a neman mu, ba a san damu ba, kuma muma ‘yan jam’iya ne. Kuma mune muka cewa mutanenmu a zaɓi jam’iyar gwamnati, domin samun zaman lafiya. Ba mu zaɓi gwamnati don a ci mutuncinmu ba ne. To wannan shi ne dalilinmu na shirya gudanar da zanga-zangar lumana.

NEPTUNE HAUSA: To kwatsam, sai muka ga sanarwar cewa an janye wannan zanga-zangar lumana da aka shirya, ko me ya faru aka janye gudanar da ita zanga-zangar?

ALHAJI NASIRU MATO: To kasan an ce wai gaba da gabanta. To daga gwamnatin jihar Yobe, aka turo mai baiwa gwamna shawara kan harkokin tsaro. Aka ƙira mu da jami’an tsaro da wakilan sarakuna da shi shugaban ƙaramar hukumar ɗin da muƙarrabansa. Muka tattauna, daga ƙarshe dai muka cimma matsaya cewa, mu, mu yi haƙuri, kar mu yi wannan zanga-zanga da muka shirya. Su ma ƙaramar hukuma su dakata da ƙudurinsu na abin da suke niyyar yi, har sai mun zo mun zauna a teburi, an warware inda matsalar take. To wannan shi ne ya sa muka janye.

NEPTUNE HAUSA: To ku yaya kuke so tsarin tafiyar da shagunan ya kasance a kasuwannin Potiskum, idan aka bawa mutum ‘allocation’?

ALHAJI NASIRU MATO: Ka ga kamar mu abin da muka sani shi ne, mun san gwamnati ta gina wurinta, kuma ta bawa mutane ‘temporary allocation’. ‘Temporary’ daman kasan cewa an baka ne na wucin gadi. Amma ita wannan babbar kasuwar ta mu yanzu haka tana da shekaru 70 da ɗoriya, kamar yadda ita kuma kasuwar NPN take da shekaru 34.

Mu fa ba ma musun cewa na wucin gadi ne. Amma wucin gadin nan sai a tambaya waye mamallakin wurin a yanzu. Mu kawai Magana muke yi a kan mamallakin wurin, kar a canza, a bar masa kayansa. Mun yarda da tsarin gwamnati, za ta iya karɓar kayanta ta ce tana so, amma a mayar wa mamallakin wurin, ai ci gaba ake so, ba wai tauye haƙƙin mutane ba, ba wai haɗa husuma ba. Mulki ai dukkanmu kafin mu zo, wasu sun yi da yawa, kuma za mu bari, tun da ba za mu mutu a kai ba.

Don haka mu a tsarin da ake tafiya, a kai muke so a tafi. Mu kawai muna so a tafi a kan tsarin da ake kai. Kana da takarda, saya ka yi ko ba ka aka yi, kai dai kai ne me shago. Ka saka kaya da kanka, ko bawa wani haya, ko kuma ka bawa wani xan’uwanka ya ci abinci, amma dai kai ne me shago.

To mu a haka muke so a tafi, kuma shi ne zaman lafiya. A babbar kasuwar Potiskum, muna da shaguna sama da dubu huɗu. A kowane shago ma ka ɗauka yana ɗauke da mutane biyar. Kai akwai shagon ma da yake ɗauke da mutane sama da goma. Yanzu mutane dubu nawa ne suke cin abinci a wannan kasuwa? A ƙalla a cikin wannan kasuwa, kullum mutane sama da dubu tara ne suke cin abinci a kullum.

A hakan ma ban da Leburori. Sannan ga shagunan cikin unguwanni, ga kuma ƙananan kasuwanni na gefe. Sannan ga Kasuwar Hatsi, ga kasuwar Shanu, ga kuma kasuwar Awaki.
Yanzu waɗannan mutane sama da dubu tara ɗin nan, idan za ka basu aikin gwamnati ina za ka saka su? Amma ba ka san a ina suke kwana ba, ba ka san yaya suke ci, suke sha, suke rayuwa ba. Ba ka sani ba, ai sun rage wa gwamnati aiki. Sannan a hakan za ka ga mutum yana da mata biyu ko uku, kuma yana da ‘ya’ya sama da goma, kuma shi yake ciyar dasu. Yanzu waɗannan ba su rage wa gwamnati aiki ba?

NEPTUNE HAUSA: Wane ƙira kake dashi ga su waɗannan masu shaguna da aka musu wannan barazana na raba su da shagunansu?

ALHAJI NASIRU MATO: Ƙira na gare su shi ne su kwantar da hankalinsu, sannan su kai hankali nesa. Don yanzu wallahi idan wani ka ƙwace masa shagonsa wallahi zai iya mutuwa, saboda hawan jini zai buge shi. Nan ne inda ya dogara da shi a rayuwarsa gaba ɗaya, da shi da iyalansa. Su kwantar da hankalinsu, a matsayinmu na shugabanni, za mu bi musu haƙƙinsu. Akwai abin da ake kawar da shi saboda maslahar al’umma. Yanzu gida na ai na kwanciya ne, idan wani abu ya taso wanda zai taimaki al’umma, kuma dole sai na ba da gida na, wallahi zan fita don a taimaki al’umma.

Sannan muna ƙara godiya ga dukkan ‘yan kasuwa, da suka kasance masu biyayya ga shugabanni. Saboda sun san muna ƙoƙarin kwatanta gaskiya. Idan muka yi ƙira, suna amsa wa. Idan muka ce a zo, suna zuwa, sannan idan kuma muka ce a tsaya suna tsayawa. Wannan babbar nasara ce. Sannan muna ƙara ƙira ga dukkan ‘yan kasuwa da su ci gaba da riƙe amana da cin halas a dukkan kasuwancin mu. Sannan mu guji haram.

NEPTUNE HAUSA: Mun gode.

ALHAJI NASIRU MATO: Nima na gode.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like