Abin da ya sa ba ma ɗaukar alƙalan wasa daga Najeriya – FIFA

0
159

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta fitar da sunayen alƙalan wasan da za su busa gasar Olympics da za a fara a watan Yuli a birnin Paris na Faransa.

Hukumar ta fitar da sunayen alƙalan wasa 12 daga ƙasashen Afrika waɗanda za su wakilci nahiyar.

Cikin alƙalan da ta fitar da sunayensu babu ɗan Najeriya ko ɗaya, duk da cewa ƙasar tana samun haɓakar ƙwallon ƙafa cikin gaggawa.

Irin wannan ce ta faru ga ƙasar a gasar cin kofin duniya da aka yi a 2022 a Qatar.

Sai dai BBC ta tattuna da wani tsohon alƙalin wasa da ya kai matakin Fifa, Ibrahim Umar Fagge kan ko me ke janyowa ana barin Najeriya a baya a irin waɗannan wasannin.

KU KUMA KARANTA: FIFA ta sanar da filin da za a yi wasan ƙarshe na gasar Cin Kofin Duniya

“Akwai dalilai da dama, na farko shi ne ko da matashi ya samu damar zama alƙalin wasan Fifa ba sa iya samun horon da ya kamata wanda zai kai shi ga fara hura wasanni a matakin manyan gasa kamar kofin duniya.

“Na biyu da yawan alƙalan suna da matsala ta rashin lafiya da ba sa iya kai wa ga inda ake so. Akwai kuma matsalar shekaru mafi yawa daga cikin mutanen namu tsofaffi ne.

“Bugun zuciyarsu da yadda jinin ke zagaye a jikinsu akwai haɗari a barsu su ci gaba da guje-guje.

“Na ƙarshe shi ne kaf Najeriya babu na’urar da ke taimakawa alƙalin wasa, wato VAR a turance,” in ji Ibrahim Umar.

A ƙa’idar Fifa mutum ba zai busa manyan gasar da ake yi ba sai ya ƙware wajen amfani da VAR.

Leave a Reply