Connect with us

Labarai

Abin da malaman kano suka faɗa kan ajiye aikin Daurawa

Published

on

Malaman Addinin Musulunci a Kano sun magantu kan murabus ɗin da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi daga mukaminsa na Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

Neptune Hausa ta rawaito a safiyar ranar Juma’a ce babban malamin ya sanar da sauka daga muƙamin a cikin wani saƙo na bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Sheikh Daurawa ya ɗauki matakin ne kwana guda bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya soki Hukumar Hisbah bisa salon ayyukanta waɗanda ya ce suna keta doka.

Sheikh Daurawa ya ce gwiwoyinsa sun yi sanyi bayan da ya saurari kalaman gwamnan kan sukar da ya yi wa Hukumar Hisbah.

Sai dai a jawabin Sheikh Daurawa, ya bai wa gwamnan haƙuri sannan ya bayyana cewa ya sauka daga muƙaminsa.

“Mun yi iya ƙoƙarinmu, mu ga cewa muna abin da ya kamata, to amma ina ba mai girma gwamna hakuri bisa fushi da ya yi da maganganun da ya faɗa.

“Kuma ina rokon da ya yi min afuwa, na sauka daga wannan mukami da ya ba ni na Hisbah, inda muka yi kuskure muna fata a yafe mana. Kuma ina yi masa masa addu’a da fatan alheri.”

KU KUMA KARANTA: Da ɗumi-ɗumi: Aminu Daurawa ya sauka daga shugabancin Hisba a jihar Kano ( Bidiyo)

Sai dai kuma a wasu bidiyoyi da suka karaɗe soshiyal midiya, malaman da suka haɗa da Sheikh Abdallah Usman Gadon Kaya da Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo, sun bayyana rashin jin daɗinsu da kuma yadda suke ganin za a tari hanzarin lamarin.

A  bidiyon farko da Dokta Gadon Ƙaya ya fitar, ya yaba wa Gwamnan Kano kan ayyukan alherin da yake kawowa jihar, da kuma ƙoƙarinsa na karɓar gyara daga al’ummarsa.

Sai dai ya ce akwai buƙatar Gwamnan ya tausasa zuciyarsa ya zauna da Malam Daurawa, domin tattaunawa da shi ya kuma ba shi haƙuri.

“Muna ƙira ga gwamna Abba Yusuf da waɗanɗa ke kusa da shi su kai zuciya nesa su kira Malam Daurawa, su zauna da shi kuma su ba shi haƙuri kan abubuwan da suka faru.”

A cikin bidiyon, Sheikh Abdallah Gadon Ƙaya ya ce ya kamata Gwamna Abba Yusuf ya duba al’ummar Jihar Kano da ci gaban da Malam Daurawa ya kawo, baya ga gudummawar da yake bai wa ita kanta gwamnatin ta Kano.

“Ya kamata a zauna da shi Malam Daurawa a ba shi shawarwari a kan abubuwan ya yake yi ko ake ta cewa Hisbah take yi,” in ji Gadon Ƙaya.

“Matsayin Malam Daurawa ya kai kuma darajarsa ta kai.”

Kazalika, Gadon Ƙaya ya kuma bai wa Sheikh Daurawa haƙuri, da kuma roƙon ya amsa kiran Gwamna idan har ya buƙaci hakan, domin ci gaban jihar da kuma kukan da al’ummar jihar ke yi saboda ajiye aikinsa.

A nasa ɓangaren, Dokta Sani Umar Rijiyar Lemo kokawa ya yi da yadda Kano ta zama cibiyar yaɗa baɗala ta dandalin sada zumunta, da kuma yadda manyan jihar suka zuba ido ba tare da ɗaukar mataki ba.

Ya bayyana cewa, “ana nema a maida Kano dandalin baɗala, dandalin fasiƙanci da fajirci! Ana tasowa daga garuruwa masu nisa a zo cikinta domin a yi baɗala.

“Ba ma garuruwa ba, har ta kai yanzu daga ƙasashe maƙota ake ƙetarowa, yarinya ta baro iyayenta, ta shigo jihar, ta kama ɗaki da gida ta fara yaɗa baɗala.

“Tiktok ɗin nan yana yi a ko’ina in dai akwai network, amma ba su yarda su yi a ƙasarsu ba, ba su yarda su yi a cikin ’yan uwansu ba, saboda suna jin kunyar ’yan uwansu ko kuma ba za su ƙyale su ba, amma za su iya takowa su zo Kano su kama gida, su riƙa yin taswirar kanta cikin ƙazantacciyar shiga, da kalamai na batsa marasa kyau, suna antayo wa ’ya’yanmu.

“Ana ji ana gani ana sane da masu yin wannan abu amma an zuba musu ido. To idan ba a tashi tsaye ba aka taka musu burki aka yi abin da ya dace ba, babu shakka idan Allah Ya tashi kama mu da azaba, ba su kaɗai zai yi wa ba. Laifinmu shi ne ba mu yi wani abu ba,” inji shi.

Haka zalika, Sheikh Rijiyar Lemo ya jaddada cewa ƙoƙarin da Hisbah ke yi na umarni da kyakkyawa da yaƙi da baɗalar ne ɗaya daga cikin abubuwan da suka sanya ake samun sauƙi a jihar.

“Jiha ce da ta kowacce fuska za a cuta idan ɓarna ta shigo saboda yawan al’umma da dukiyar da ke ciki, amma Allah Ya tsare ta.”

Ya kuma ja hankalin gwamnati, da shugabanni, da sarakuna, haɗi da sauran malaman jihar kan illar zuba ido hakan ta ci gaba da faruwa, domin a cewarsa azabar da za ta game kowa ce a ƙarshe za ta faɗowa al’umma.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like