A lissafin da na yi, Tinubu na uku zai zo a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 – El-Rufai

0
415
A lissafin da na yi, Tinubu na uku zai zo a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 - El-Rufai
Elrufai da shugaban ƙasa Tinubu

A lissafin da na yi, Tinubu na uku zai zo a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 – El-Rufai

Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai zo na uku ne a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 mai zuwa.

El-Rufai jigo a jam’iyyar ADC, ya bayyana cewa Tinubu zai sha kashi a zaɓen 2027 idan ya tsaya takara, inda ya ce mafi yawan abin da zai samu shi ne zuwa na uku a zagaye na farko wanda hakan zai kai ga sake zaɓen ba tare da shi ba.

El-Rufai ya bayyana haka a tattaunawa da tashar Channels a ranar Lahadi, inda ya shawarci Tinubu da ya ɗauki darasi daga tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar a zaɓen 2015.

Ya ce: “Idan kana son ka yaudari kanka, kana da ‘yanci. Ba zan gaya maka yadda za mu yi nasara ba, amma zan faɗa maka a sarari cewa a mummunan yanayi mafi tsanani a zaɓen 2027 babu wanda zai lashe shi a zagaye na farko.

KU KUMA KARANTA: El-Rufai ya kai ƙarar Majalisar Dokokin Kaduna kotu

“Za a iya komawa zuwa zagaye na biyu, kuma Bola Tinubu ba zai kasance a cikin ‘yan takara ba, domin mafi yawan abin da zai iya samu shi ne na uku. Babu hanyar da zai yi nasara. Na yi lissafi, na yi nazari; ba zai iya lashewa ba, mafi yawan abin da zai iya samu shi ne na uku.

Ya zargi Shugaban ƙasa da lalata tattalin arziƙin ƙasa, yana mai cewa mutane miliyan 30 sun shiga cikin ƙangin talauci a cikin shekaru biyu da suka wuce sakamakon manufofin tattalin arziƙin gwamnatin Tinubu.

El-Rufai, wanda dangantakarsa da Tinubu ta yi tsami bayan Majalisar Dattawa ta yi watsi da naɗinsa a matsayin minista, ya ce da an naɗa shi minista a gwamnatin Tinubu, da ya yi murabus.

Leave a Reply