A karon farko jam’iyya mai mulki a Japan ta zaɓi mace a matsayin jagorarta
Jam’iyyar da ke mulkin Japan ta zaɓi tsohuwar ministar tattalin arziki ta ƙasar, Sanae Takaichi a matsayin sabuwar jagorarta a Asabar, lamarin da ya ɗora ta akan turbar kasancewa mace ta farko da ta riƙe muƙamin Firaminista a ƙasar.
RFI ta ruwaito cewa a cikin ƙasar da ta yi kaurin suna wajen hana mata rawar gaban hantsi a fannin siyasa sakamakon rashin daidaito, Takaichi, za ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta jagoranci jam’iyyar da ta daɗe tana mulkin ƙasar.
Tana ɗaya daga cikin mambobin jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya.
Takaichi ta doke ministan noma na ƙasar Shinjiro Koizumi, wanda ɗa ne ga tsohon Firministan ƙasar, Junichiro Koizumi.
KU KUMA KARANTA: Japan ta jaddada goyon bayanta ga Ukraine akan mamayar da Rasha ta yi mata
Za a kaɗa ƙuri’a a ranar 15 ga wannan wata na Oktoba domin zaɓen wanda zai zama firaminista a majaalisar dokokin ƙasar.
Ana sa ran Takaichi ta maye gurbin firaminista Shigeru Ishiba ganin cewa jam’iyyar LDP mai mulki ce mafi girma a majalisar dokokin ƙasar. Sai dai bayan koma baya da jam’iyyar ta samu a manyan zaɓuka, yaanzu LDP ba ta da rinjaye a majalisar dokoki biyun, saboda haka za ta nemi goyon bayan ‘yan adawa a majalisar domin guanar da mulki mai inganci.









