A dakatar da batutuwan siyasa sai bayan Azumi – shugaban jami’iyar APC a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Shugaban Jami’iyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas Sanusi ya yi ƙira da a tsagaita wutar siyasa zuwa bayan watan Ramadan.
Abdullahi Abbas ya yi wannan ƙira ne a lokacin da yake rabon kayan azumi a gidansa, inda ya ce
KU KUMA KARANTA:Yadda babban taron APC na ƙasa ya gudana a Abuja
“Ina kira ga Yan siyasa da cewar mu dakatar da batutuwan Siyasa sai zuwa bayan a zumi” a cewar Abdullahi Abbas
“Yan siyasa da attajirai ku fito ku rabawa mabukata abincin da za su ci, ba dole sai irin abinda Abdullahi Abbas ya raba ba, zaku iya yin sama da nashi ko kasa da nashi” inji abdullahi abbas.