Juyin mulkin Guinea Bissau ya fi min ciwo fiye da shan kaye a zaɓen 2015 – Jonathan
Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa juyin mulkin da ya faru a Guinea Bissau ya fi masa ciwo fiye da lokacin da ya kira Muhammadu Buhari ya taya shi murna a zaben 2015 da ya sha kaye.
A cewarsa, lamarin ya taba shi sosai domin ya dade yana taka rawa wajen dawo da dimokuradiyya a kasar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A lokacin rikicin, Jonathan ya je Guinea Bissau ne a matsayin wakilin kungiyar dattawan Yammacin Afrika don sa ido kan zaben kasar, tare da tawagogin AU da ECOWAS. Sai dai kafin su kammala aikinsu, rundunar soji ta kwace mulki, lamarin da ya bar shi da tawagarsa cikin fargaba har aka kwashe su aka dawo da su Nijeriya ranar Alhamis.
KU KUMA KARANTA: Cikar Najeriya shekaru 65: Jonathan ya hori ‘yan ƙasar da ka da su fidda rai da samun ci gaba
Jonathan ya ce abin ya daga masa hankali sosai saboda bai taba tunanin zai tsinci kansa a irin wannan yanayi ba.
Hakazalika ya kara da cewa, abin da ya faru a Guinea Bissau ya fi masa ciwo fiye da ranar da ya kira Buhari bayan ya sha kaye a zabe, domin shi mutum ne da yake da yakinin dimokuradiyya.









